✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP na iya sake faduwa a Zamfara idan ta tilasta ’yan takara – Milo

Alhaji Nasiru Abubakar Milo dan siyasa ne da ke tare da jama’arsa, kuma a yanzu yana sha’awar tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya daga mazabarTsafe/Gusau a…

Alhaji Nasiru Abubakar Milo dan siyasa ne da ke tare da jama’arsa, kuma a yanzu yana sha’awar tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya daga mazabarTsafe/Gusau a Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar PDP. A tattaunawrsa da Aminiya ya ce PDP tana iya sake rasa jihar a zaben badi idan shugabannin jam’iyyar na kasa suka tilasta wa jama’ar jihar ’yan takarar da ba dace ba:
Kwanakin baya Shugaba Goodluck Jonathan a wurin gangamin shiyya na Jam’iyyar PDP ya ce jam’iyyar za ta lashe zaben Jihar Zamfara a badi, ta yaya hakan zai yiwu?
Ko shakka babu jam’iyyarmu ta PDP ta kama kasa a Jihar Zamfara, kuma idan zaben badi ya zo mutane na shirye su hada hannu da jam’iyyar don ta kafa gwamnati, saboda sun gwada ’yan adawa sun gaza bunkasa jihar. Yanzu kai ya waye, ba wanda zai yaudari jama’a da APC ko wakilanta da babu wata gudunmawa da suka bayar wajen samar da ribar dimokuradiyya ga jama’a.
Wane tabbaci kake da shi cewa a wannan karo za ku samu nasara, saboda Jihar Zamfara ta ki rungumar PDP tun 1999?
Yanzu tsoron da kawai muke ji, shi ne tsoro da jita-jitar tilasta ’yan daga uwar jam’iyya da ke Abuja.  Kada shugabanninmu a matakin kasa su kuskura su yi haka. Maimakon haka su bayar da dama ga dukkan masu son tsayawa takara su baje kolinsu a kuma kyale jama’a su zabi wanda suke so ya zama dan takarar Gwamna da sauran mukamai.
Me ya sa kake fadin haka a yanzu da ake da sauran watanni kafin zaben share-fage?
Saboda mun ji ana zargin cewa daya daga cikin masu son tsayawa takarar Gwamna a Jihar Zamfara kuma Minista a Ma’aikatar Ayyuka Ambasada Bashir Yuguda yana fada wa mutane cewa shi aka riga aka ajiye wa kujerar takarar, kuma matar Shugaban kasa Misis Patience Jonathan ta yi alkawarin taimaka masa ya samu tikitin PDP, wai saboda kusancinsa da Uwargidan Shugaban kasar.  
Idan wannan jita-jita ta tilasta dan takara ta tabbata, me kake hange hakan zai jawo wa PDP a zaben 2015 a Jihar Zamfara?
Shawarar da zan ba Uwargidan Shugaban kasa Misis Patience Jonathan ita ce ta cire hannunta daga batun zaben share-fage na dan takarar Gwamnan Zamfara ta bar jama’ar jihar su zabi ’yan takarar da za su iya cin zabe, domin yin sabanin haka babu shakka zai kawo cikas ga kokarin da shugabannin jam’iyyar suke yi na ganin PDP ta lashe zaben badi. Abin da mutanen Zamfara suke gani, idan Uwargidan Shugaban kasa ta tilasta Bashir Yuguda a kan mutanen Zamfara, zai haifar da bakin ciki, domin zai sa a kada PDP a cikin ruwan sanyi a zaben badi, saboda ba wanda ya san shi a siyasance a yankunan karkara. Wannan zai jawo wa jam’iyyar jangwam a Zamfara, domin jiharmu ta bambanta da Jihar Ribas da ma sauran jihohi. Jama’ar Zamfara sun san wanda suke so, sun san su wane ne shugabanninsu, kuma za su yi amfani da karfin kuri’arsu su ki zaben duk wani dan takara da aka tilasta musu da bai da goyon bayansu.
Amma Ministan ya dade a cikin harkar siyasa na wani lokaci, me ya sa ka ce ba ya da goyon baya a wajen mutanen karkara?
Bari in maida ka baya game da tarihin siyasar Jihar Zamfara. Babu shakka PDP ta sha kasa a hannun ’yan adawa a zabubbuka hudu da suka gabata. Kuma PDP za ta lashe zaben badi ne kawai a Jihar Zamfara idan ta bayar da dama tare da kyale jama’a su zabi wanda suke so, musamman ta guji duk wani rudi na kokarin tilasta wa jama’a ’yan takara.   
Lokaci ya yi da za a kauce wa wannan dabi’a idan muna son wannan jam’iyya tamu mai girma ta samu nasara a zaben badi. Ko shakka babu idan aka bari gogagge kuma dan takarar da ke da goyon baya a wurin jama’ar karkara, dan takarar da aka fi so kuma yake da goyon bayan jama’ar Zamfara ya ci zaben share-fage, to jam’iyyarmu ta PDP za ta lashe zaben Jihar Zamfara a badi. Akwai jita-jitar da ake yadawa cewa hatta Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara da magoya bayansa suna addu’ar PDP ta tilasta Bashir Yuguda a matsayin dan takararta, domin hakan zai sa jam’iyyar adawa ta samu nasara cikin sauki a zaben badi a Jihar Zamfara. Sarkakiyar da ke cikin lamarin ita ce abin takaici shi ne Ministan ba ya da abin da ake bukata da karfin da zai iya cin zabe a jihar.
Wane kokari ne kake jin shugabannin PDP ke yi don tabbatar da jam’iyyar ta samu nasara a zabubbukan badi?
Hakika Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Ahamdu Adamu Mu’azu yana dora jam’iyyar a kan ginshiki mai karfi da babu shakka zai jawo hankalin ’yan siyasa masu nagarta da za su sa ta samu nasara a zaben badi da zabubbuka na gaba. Abin da kawai shugabannin jam’iyyar suke bukata shi ne hadin kanmu, su kuma su guji dora ’yan takarar da jama’a ba su so ta kowace hanya.