Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya ce gazawar jam’iyyar PDP wajen gyara matatun man Najeriya tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki ne ya kawo karancin mai da ake fama da shi a yanzu.
A tattaunawarsa da wani gidan talabijin a Najeriya, Oshiomhole, wanda shi ne Mataimakin Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima, ya zargi PDP da lalata matatun man kasar.
- Fintiri ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin ayarin motocinsa
- Wahalar mai: Gwamnati ta zargi ’yan kasuwa da boye fetur
“Mu tambayi kanmu, waye ya lalata matatun man tun farko? Yaya yanayinsu yake a shekarar 1999, da kuma daga wannan lokacin zuwa 2015?
“Idan PDP da ta yi mulkin shekara 16 ta gaya wa ’yan Najeriya kudin da suka barnatar wajen kula da wadannnan matatun sai ’yan Najeriya sun suma saboda yawa.
“Haka kawai (Olusegun) Obasanjo ya yanke shawarar cefanar da matatun mai, amma wanda ya gaje shi da ya zo sai ya yi mi’ara koma baya, saboda a cewarsa a watanni shida za a samu mai a wancan lokacin, wannan shi ne tushen matsalar da muka samu kanmu a ciki,” inji shi.
Don haka ya ce ya zama dole a yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari bisa samar da sabuwar dokar man fetur da kuma jawo hankalin masu zuba jari da suka dace a bangaren, ciki har da matatar man Legas mallakin hamshakin attajirin Afirka, Aliko Dangote.