✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ba za ta iya karbe Jihar Legas-APC

  Jam’iyyar APC jiya ta bayyana jam’iyyar PDP a matsayin “matacciyar jam’iyya wacce ba za ta iya karbe Legas ba a zaben shekarar 2019."  …

 
Jam’iyyar APC jiya ta bayyana jam’iyyar PDP a matsayin “matacciyar jam’iyya wacce ba za ta iya karbe Legas ba a zaben shekarar 2019."
 
Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC a jihar Legas, Mista Abiodun Salami ne ya yi furucin a tattaunawar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Jihar Legas.
 
Salami ya yi furucin ne yayin da yake mayar da martani ga furucin da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na jihar Legas, Mista Taofik Gani ya yi inda ya ce jam’iyyar adawa za ta lashe zaben Legas kuma za ta karbe gwamnatin a shekarar 2019.


%d bloggers like this: