Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmad Bala Ngillari, ya ce jam’iyyar adawa ta PDP ta mutu, kuma ba ta da makoma a Najeriya.
Ngilari ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ya gudana a Yola, ranar Asabar.
- Kayan tallafi: Gwamnan Adamawa ya yi barazana ga rayuwar matashi
- APC ta yi mana fashi a zaben kananan hukumomin Adamawa – PDP
- Sanata Elisha Abbo ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC
“Dalilin da yasa na sauya sheka daga PDP zuwa APC, shi ne saboda PDP ta mutu.
“Abu na biyu, kuma ban ga wata hanya mai billewa ga ‘ya’yan jam’iyyar ba.
“Abin da ya sa na dawo APC shi ne saboda na fuskanci ita ce za ta kai mu tudun mun tsira a kasar nan.”
Tsohon gwamnan, ya yi takarar kujerar Sanata a jam’iyyar PDP a zaben 2019, kafin komawarsa APC a 2020.
Ya kara da cewa duk mai kishin cigaban Najeriya ya kamata ya shiga jam’iyyar APC.
A cewarsa, ita ce jam’iyyar da za ta kawo mafita ga Najeriya da talakawanta.
Ngillari ya ba wa ‘yan jam’iyyar APC a Adamawa tabbacin cewa jam’iyyar ce za ta lashe kaso 90 na zaben 2023.