Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya janye takunkumin da aka sanya kan sayarwa da kuma sabunta layukan waya a Najeriya.
Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya sanar a ranar Alhamis, cewa za ci gaba da sauran abubuwan da a baya aka dakatar, muddin aka kiyaye dokokin da ma’aikatarsa da bayar na amfani da lambar NIN.
- ’Yan bindiga sun kai hari dab da barikin soja da ke Jaji
- Na rabu da mai neman aurena kan raina Kwankwaso —Budurwa
- Yadda ’yan daban daji 30 suka fada tarko a Katsina
Ya za a ci gaba da yin rajistar sabbin layin ne bayan Shugaba Buhari ya amince da sabon tsarin rijistan layuka da ma’aikatar ta bullo da shi.
Ya ce tsarin ya “wajabta amfani da lambar NIN wurin yin rajistar sabon layi a ranar 14 ga Afrilu, 2021,” inji sanarwar.
Ya kara da cewa, “Sabon tsarin ya shafi sayen sabbin layin waya, bude su da kuma maye gurbinsu na kamfanoni da hukumomi da sauransu. Kuma mallakar lambar NIN sharadi ne a kowane rukuni.