✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pantami ya ba Airtel kwana uku ya gyara matsalar sadarwa

Gwamnatin Tarayya ta ba wa kamfanin sadarwa na Airtel wa’adin kwanaki uku ya gyara hanyoyin sadarwarsa tare da warware matsalolin jama’ar da ke hulda da…

Gwamnatin Tarayya ta ba wa kamfanin sadarwa na Airtel wa’adin kwanaki uku ya gyara hanyoyin sadarwarsa tare da warware matsalolin jama’ar da ke hulda da shi.

Ministan  Sadarwa da Tattalin Arzikin, Dakta Isa Ali Pantami ya sanar da haka ta shafinsa na Twitter.

Pantami ya umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) umarnin bincikar lamarin inda ya ce “na samu korafe-korafe a kan kamfanin Airtel kuma ina so ku yi bincike tare da gabatar min da sakamakon binciken cikin kwanaki 3 sannan a kuma a tabbatar an warware matsalolin da abokan hulda da kamfanin ke fuskanta”, inji Pantami.

A cikin karshen makon jiya ne mutane da dama suka shiga bayyana korafinsu kan Airtel musamman a Twitter tare da neman dauki daga Ministan.