Gwamnatin Tarayya ta ba wa kamfanin sadarwa na Airtel wa’adin kwanaki uku ya gyara hanyoyin sadarwarsa tare da warware matsalolin jama’ar da ke hulda da shi.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin, Dakta Isa Ali Pantami ya sanar da haka ta shafinsa na Twitter.
- Airtel ya samar da layin waya don yaki da mace-macen mata
- NCC ta ci tarar kamfanin CWG Naira miliyan 25
- Hukumar NCC ta kai karar mutum 7 bisa satar fasaha
- NCC za ta sake bunkasa harkar kula da abokan hulda
Pantami ya umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) umarnin bincikar lamarin inda ya ce “na samu korafe-korafe a kan kamfanin Airtel kuma ina so ku yi bincike tare da gabatar min da sakamakon binciken cikin kwanaki 3 sannan a kuma a tabbatar an warware matsalolin da abokan hulda da kamfanin ke fuskanta”, inji Pantami.
A cikin karshen makon jiya ne mutane da dama suka shiga bayyana korafinsu kan Airtel musamman a Twitter tare da neman dauki daga Ministan.