✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pantami da Adam Zango sun zama Daraktocin Qausian TV

Tsohon Gwamnan Kano, Kanar Sani Bello murabus ya zama shugaban majalisar daraktocin Qausain TV

An naɗa tauraron masana’antar Kannywood kuma mawaƙi, Adam A. Zango a matsayin Darakta-Janar na gidan talabijin na Qausain TV.

Rukunin kamfanin ya kuma naɗa  tsohon Gwamnan Jihar Kano, Kanar Sani Bello (murabus) a matsayin shugaban Majalisar Daraktoci.

Shugaban Qausain TV, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani), ya kuma sanar da naɗin tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami tare da ƙwararren ɗan jarida kuma tsohon ma’aikacin BBC, Ahmad Abba, a matsayin daraktoci da ba na gudanarwa ba.

Albani ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa da ƙwarewar sabbin daraktocin, za su samar da kyakkyawan jagoranci tare da inganta cigaban ayyukan kamfanin.

Ya bayyana cewa naɗin Kanar Sani Bello ya jagoranci majalisar daraktocin Qausain ne na tsawon shekaru huɗu, yana da muhimmanci wajen samar da kyakkyawan jagoranci da kawo cigaba a fannin watsa labarai.

Sanarwar ta ƙara da cewa Majalisar Daraktocin kamfanin ta amince da naɗe-naɗen a zamanta na ranar 4 ga watan Oktoba, 2024.