✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ozil zai ci gaba da zama a Arsenal

Mesut Ozil, dan asalin Jamus kuma tsohon dan kwallon kulob din Madrid na Sifen a shekaranjiya Laraba ne ya yanke shawarar ci gaba da zama…

Mesut Ozil, dan asalin Jamus kuma tsohon dan kwallon kulob din Madrid na Sifen a shekaranjiya Laraba ne ya yanke shawarar ci gaba da zama a kulob din Arsenal da ke Ingila.

An yi ta rade-radin dan kwallon yana yunkurin barin kulob din bayan kulob din ya kasa hayewa gasar cin kofin zakarun kulob na Turai a bana, amma wannan kalami da ya yi, ya kawo karshen rade-radin.

Dan kimanin shekara 28, Ozil ya ce da zarar kulob din ya kammala balaguron da ya tafi kasashen Austireliya da Chaina don yin wasannin sada zumunta kafin a fara kakar wasa ta bana, zai zauna da mahukunta kulob din don ya sanar da su aniyarsa ta ci gaba da zama a kulob din.

“Na sha nanata cewa ina jin dadin zama a kulob din Arsenal, kuma ko shakka babu zan ci gaba da zama a kulob har zuwa badi, hasalima ban san lokacin da zan bar kulob din ba.  A yanzu dai na fi mayar da hankali ne a wasannin sada zumuntar da muka fara a shirye-shiryen tunkakar kakar wasa ta bana, amma yanzu na yanke shawarar ci gaba da zama a kulob din”.

A jiya Alhamis ne kulob din Arsenal ya fara wasan sada zumunta da kulob din Sydney na Austireliya.  Sannan nan gaba kadan kulob din zai hadu da na Bayern Munich da kuma na Chelsea duk a wasannin sada zumunta.