dan wasan tsakiya a kulob din Real Madrid da ke Sifen Mesut Ozil a shekaranjiya Laraba ne ya karyata rade-radin da ake yi cewa akwai yiwuwar zai bar kuulob din kafin a rufe kakar saye da sayar da ’yan wasa ta bana.
Rahotanni sun nuna kulob din Manchester United da na Arsenal dukkaninsu da ke Ingila sun yi ta rububin dan kwallon don ganin sun saye shi daga Madrid a ’yan kwanakin nan ganin yadda matashin dan kwallon dan kimanin shekara 24 ganin yadda kulob din yake ajiye shi a benchi.
Sai dai fitowar dan kwallon ya yi a kafafen watsa labarai a shekaranjiya Laraba inda ya nuna ba shi da niyyar barin kulob din Madrid ta sa kungiyoyin kwallon kafar da suke zawarcinsa gwiwoyinsu yin sanyi.
“”Ina jin dadin zama a kulob din Madrid kuma kwantaraginsa a kulob din ba zai kare ba sai a shekarar 2016, a gaskiya ba ni da niyyar barin kulob din a halin yanzu”, inji Ozil a lokacin da yake hira da manema labarai.
Ozil ya koma kulob din Madrid daga na Werder Bremen da ke Jamus ne a shekarar 2010.
Ozil ya karyata rade-radin barin kulob din Real Madri
dan wasan tsakiya a kulob din Real Madrid da ke Sifen Mesut Ozil a shekaranjiya Laraba ne ya karyata rade-radin da ake yi cewa akwai…