Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar wa Aminiya.
A cewar majiyoyin, Osinbajo na son karbar ragamar Shugabancin kasar ne bayan karewar wa’adin Buhari a 2023 don dorawa kan nasarorin da suka samu bayan karbar mulkinsu daga PDP a 2015.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Najeriya Miliyan 19 Za Su Rasa Abinci —Rohoto
- NDLEA ta kama babban limami da kunshin wiwi 54 a Legas
Kodayake har yanzu bai bayyana aniyarsa tasa a hukumance ba, hakan na nufin ke nan zai fafata da jagoran jam’iyyar APC na kasa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, wanda shi ma a ’yan watannin baya ya ziyarci Buharin sannan ya shaida masa aniyarsa ta tsayawa takarar.
“Tabbas Osinbajo ya shaida wa Buhari yana so ya gaje shi,” inji daya daga cikin majiyoyin.
“Da farko sai da ya tuntubi wasu fitattun ’yan Najeriya wadanda suka karfafa masa gwiwar cewa ya fada wa Buharin da kansa.
“Sun shawarce shi kada ya bari Shugaban ya ji a bakin wani, don kada a samu matsala,” inji majiyar.
Kazalika, wata majiyar ta ce lokacin da Osinbajon ya tunkari Buhari da maganar, bai nuna mamaki ba.
“Buhari ya yi murmushi, irin wanda ya saba…ya saurare shi a tsanake, sannan lokacin da zai mayar da martani, sai ya yi masa fatan alheri, ba tare da ba shi wani tabbacin fifita shi a kan sauran masu zawarcin kujerar ba.
“Ya yi masa fatan alheri kamar yadda ya yi wa Tinubu lokacin da ya ziyarce shi a Fadar Shugaban Kasa don samar masa da aniyarsa.
“Kuma ina tunanin Shugaban na yin taka-tsantsan ne. Ka tuna abin da ya fada yayin wata tattaunawa da aka yi da shi kwanaki a gidan talabijin?,” inji majiyar.
Kodayake Osinbajo, wanda lauya ne kuma dan siyasa, bai fito karara ya bayyana aniyar tsayawa takarar a hukumance ba, amma kungiyoyi da dama sun bayyana da ma wasu daidaikun mutane suna goya masa baya.
Kungiyoyin dai sun jima suna karade sassa daban-daban na kasar nan suna nema masa goyon baya da kuma daukar nauyin tallace-tallace a kafafen yada labarai.