✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osaze Odemwingie ya zama angon karni

Shahararren dan kwallon Najeriya Osaze Odemwingie ya zama angon karni bayan da matarsa Sarah ta haifa s’ya mace da suka sanya mata suna Sophia. Ma’auratan…

Shahararren dan kwallon Najeriya Osaze Odemwingie ya zama angon karni bayan da matarsa Sarah ta haifa s’ya mace da suka sanya mata suna Sophia. Ma’auratan sun bayyana farin cikinsu kan karuwar a shafinsu na Twitter a ranar Litinin da ta gabata.
Osaze ya aika da wani sako da ke cewa “Ina mai sanar da ku cewa mai dakina ta haifar mini ’ya mace da muka sanya mata suna Sophia.  Muna yi wa Allah godiya a kan wannan kyauta da Ya ba mu, kuma jaririyar da mahaifiyarta suna cikin koshin lafiya.”  Wannan shi ne karo na uku da matarsa ke haihuwa.
Osaze ya yi wasa a kulob da dama da suka hada da Bendel Insurance a Najeriya da Lille na Faransa da Locomotibe na Mosko da West Brom Albion da Cardiff City da Stoke City na Ingila.  Kuma yanzu yana kwallo ne a kulob din Bristol da ke yin wasa a rukunin ’yan dagaji na Ingila a matsayin aro daga kulob din Stoke City.
Ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasanni 68 inda ya samu nasarar zura kwallaye 10 a raga. Yanzu haka dan kwallon yana da shekara 35 ne a duniya al’amarin da ya sa ake ganin ya fara tsufa a fagen kwallo.