✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ooni na Ile-Ife ya ba ’yan Arewa a Ife kasuwa

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan Arewa mazauna garin Ile-ife suka yi bikin bude sabuwar kasuwarsu da babban basaraken nan na lardin Yarabawa…

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan Arewa mazauna garin Ile-ife suka yi bikin bude sabuwar kasuwarsu da babban basaraken nan na lardin Yarabawa ya ba su, wato Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi; a yunkurinsa na kawar da zaman kashe wando a tsakanin al’ummar masarautarsa da ma daukacin ’yan Najeriya.
Sarkin Hausawan Ile-ife Alhaji Mahmuda Lawal Madagali ya shaida wa Aminiya cewa Ooni na Ile-ife na yunkurin kawar da zaman banza, don a halin yanzu yana gina wasu manya-manyan manana’antu, ya kuma yi alkawarin tuntubar masarautar ’yan Arewa mazauna jihar domin bai wa jama’arsu guraban ayyuka.  “Ya tamabaye mu a ina kasuwar ’yan Arewa take a Ile-ife?  Sai na fada masa ai yanzu mu ba mu da kasuwa a Ife. Nan take ya sa aka ba mu filin wata tsohuwar sitadiyom da aka rushe, sai ya ce nan ya kamata a ba mu mu yi kasuwa, in ya so shi zai ba da wani wajen da za a yi sabuwar sitadiyom.” Inji shi.
Shugaban Matasa na Ile-ife Malam Ahmad Salihu ya shaida wa Aminiya cewa akwai kasuwar goro da ’yan Arewa ta ’yan Arewa a farkon zamansu, domin goron ne ya kawo su shekaru aru-aru; sai dai rashin samuwar goron ne ya sa kasuwar ta watse amma wannan sabuwar kasuwa ta kunshi kayayyaki da suka kunshi na abinci da kayan marmari irin kankana da shanu da tumaki. “Don haka muna kira ga dukkanin ’yan kasuwa na Arewaci da Kudancin kasar nan da su shigo wannan sabuwar kasuwa domin su ci gajiyarta.” Inji shi.
Alhaji Abdulhamid Muhammad shugaban kungiyar dilallan ma’adanai na Jihar Osun ya shaida cewa Jihar Osun jiha ce da dubban ’yan Arewa ke amfana da ayukkan yi ta hanyar ayyukan da suke yi a wuraren hakar ma’adanai baya ga kasuwanci da suke yi a jihar.