✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Onazi ya sadaukar da kwallonsa ga harin bam na Abuja

dan kwallon Najeriya da ke yin wasa a kulob din Lazio da ke Italiya Ogenyi Onazi a ranar Litinin da ta gabata ne ya sadaukar…

dan kwallon Najeriya da ke yin wasa a kulob din Lazio da ke Italiya Ogenyi Onazi a ranar Litinin da ta gabata ne ya sadaukar da kwallon da ya zura a ragar kulob din Napoli a gasar rukunin Serie A ta Italiya ga wadanda harin bam din Abuja ya rutsa da su a ranar Litinin da ta gabata.
Harin bam din ya auku ne a wata tashar mota da ke Nyanya kusa da garin Abuja inda ya halaka akalla mutum 71 sannan fiye da 150 suka samu raunuka.
Onazi ya ce ya yi  bakin cikin faruwar al’amarin don haka ne ya sadaukar da kwallon da ya jefa a ragar Napoli ga wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata.
Shi dai Onazi yana daga cikin ’yan kwallon da suke buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles.  Yana daya daga cikin wadanda ake sa ran za su wakilci kasar nan a gasar cin kofin duniya da zai gudana a kasar Brazil a watan Yuni mai zuwa.