✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Omicron ta rage armashin bikin Kirsimeti a bana

Tsirarun mutane sun gudanar da taron addu’a a birnin Bethlehem, al’amarin da ba a saba ganin haka ba.

Miliyoyin  al’umma a sassan duniya sun fara gudanar da bikin Kirsimeti a daidai lokacin da sabon nau’in cutar Coronavirus na Omicron ke ci gaba da yaduwa, lamarin da tun kafin yanzu aka yi hasashen zai rage armashin bikin a bana.

Duk da yake akwai mutane da dama da za su gudanar da bikin na Kirsimeti a killace a gidansu domin kauce wa kamuwa da annobar ta Coronavirus, la’akari da nau’in Omicron wanda aka ce yana da wuyan sha’ani.

A yanzu dai shekaru biyu kenan a jere da juna da wannan annoba ta Coronavirus na kawo cikas ga bikin na Kirsimeti.

A can Bethlehem kuwa, wurin da mabiya addinin Kirista suka yi amanna cewa, nan ne mahaifar Annabi Isa Alaihi-s-salatu wassalam, masu gidajen otel-otel sun shiga damuwa saboda karancin baki da cutar ta Coronavirus ta takaita adadinsu a bana, yayin da kuma Isra’ila ta rufe kan iyakokinta.

Tun a tsakar daren Juma’a, wato jajibirin ranar bikin na Kirsimetin, tsirarun mutane ne za su gudanar da taron addu’a a birnin na Bethlehem, al’amarin da ba a saba ganin haka ba kamar yadda Rediyon Faransa ya ruwaito.

Gwamnatocin kasashen Turai sun kafa wasu tsauraran ka’idojin yaki da cutar ta Coronavirus, lamarin da ya rage wa bikin na Kirsimeti armashi.

Kasashe irinsu Netherlands da Spain da Italiya duk sun wajabta sanya takunkumin rufe baki da hanci musamman a bainar jama’a da zummar takaita yaduwar annobar a lokacin bikin na Kirsimeti.

A soke shagulgulan Kirsimeti don dakile yaduwar Omicron

Tun karatowar wannan lokaci Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukaci jama’a su soke shagulgula ko tafiye-tafiyen da suka tsara a lokutan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara saboda tsanantar cutar Coronavirus nau’in Omicron da ka iya kara tsananta a irin wannan lokaci.

A cewar hukumar nau’in Kwarona na Omicron yana yaduwa kamar wutar daji fiye da yadda aka ga yaduwar nau’in Delta da ya gabata, kuma yakan harbi hatta mutanen da suka karbi cikakkiyar riga-kafi ko wadanda suka warke daga cutar ta Coronavirus.

Darakta Janar na Hukumar Lafiyar Mista Tedros Adhanom Gebreyesus ya ce abin fargaba ne yadda nau’in na Omicron ke saurin bazuwa tare da harbar hatta wadanda suka yi jinyar cutar a baya ko kuma suka karbi cikakkiyar riga-kafi.