✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Olukayode Ariwoola: Wane ne sabon Alkalin Alkalan Najeriya?

Ariwoola shi ne alkali mafi girman mukami bayan murabus din Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad.

A ranar Litinin ce Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya.

An nada sabon Babban Jojin kasar ne sakamakon murabus din da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi bisa dalili na rashin lafiya.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola shi ne ke bi wa babban jojin Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad baya.

A ranar Litinin din ce aka wayi gari da labarin murabus din Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad cikin wata sanarwar da mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai Isa Ahuraka ya fitar.

Ahuraka ya ce tun a ranar Lahadi Mai Shari’a Tanko ya ajiye aikin nasa.

Mai Shari’a Olukayode Ariwoola shi ne alkali mafi girman mukami bayan murabus din Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad.

Haihuwa da Karatunsa

An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1954 a Jihar Oyo.

Babban Jojin ya fara karatunsa ne a Karamar Hukumar Iseyin ta jihar Oyo daga 1959 zuwa 1967.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola yayin shan rantsuwar kama aiki

Ariwoola ya kammala digirinsa a fannin shari’a a Jami’ar Ife wacce ta zama Jami’ar Obafemi Awolowo a Ile Ife da ke Jihar Osun a 1980.

Mai shari’a Ariwoola ya yi karin karatuttuka da kuma kwasa-kwasai a kasashe daban-daban bayan Najeriya da suka hada da Birtaniya da Faransa da Amurka da Birtraniya da UAE.

Aiki da daukaka

Ariwoola ya yi alkalanci a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, kafin ya samu daukaka zuwa Kotun Kolin kasar, inda ya shafe kusan shakara 11 a matsayin daya daga cikin manyan Alkalan Kotun Kolin, bayan shigarsa cikinta a watan Nuwamban 2011.

Kafin ya zama alkalin Kotun Koli dai yana Kotun Daukaka Kara ne a matsayin daya daga cikin alkalanta, sakamakon karin girma da ya samu daga Babbar Kotun Jihar Oyo.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola tare da Shugaba Muhammadu Buhari bayan shan rantsuwa

Sannan ya rike matsayin alkali a Kotunan Daukaka Kara na Kaduna da Enugu da kuma Legas.

A yanzu bayan rantsar da shi, ya zama baban jojin Najeriya na 18, kuma ga alama shi ne zai ja ragamar yanke hukuncin shari’ar Zaben Shugaban Kasa na 2023 idan har an samu korafi bayan zaben.

Gwagwarmaya

Mai shari’a Ariwoola na daya daga cin alkalai bakwai na Kotun Koli da suka yanke hukunci kan karar zaben Shugaban Kasa na 2019 da suka tabbatar da Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu.