✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ogun ta shirya don gudanar da Gasar Wasanni ta Kasa a 2022 – Kwamishina

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Dokta Oluwadare Kehinde, ya ce jihar a shirye take tsaf ta dauki nauyin Gasar Wasanni ta Kasa karo 21…

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Dokta Oluwadare Kehinde, ya ce jihar a shirye take tsaf ta dauki nauyin Gasar Wasanni ta Kasa karo 21 da za a gudanar a shekarar  2022. Aminiya ta kalato cewa za a sanar da inda za a gudanar da gasar karo na 21 ne lokacin bikin rufe gasar karo na 20 da za a fara a wannan wata a Jihar Edo.

Dokta Oluwadare Kehinde ya bayyana ne a yayin da Kwamitin Tattancewa daga Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Kasa ya kai ziyarar gani-da-ido don tatance filayen wasanni da kayan wasa a Jihar Ogun.

Kwamishina Kehinde wanda ya zagaya da ’yan kwamitin don tantance kaya da filayen wasanni a garin Abeokuta da Shagamu da Ijebu-Ode ya bayyana shirin Jihar Ogun don ganin ta dauki nauyin gasar a shekarar 2022. Ya bayyana cewa jihar tana matukar ba harkar wasanni goyon baya don ganin ta inganta ta.

Da yake tofa albarkacin bakinsa bayan sun gama kewayawa, Shugaban Kwamitin Tantanceawar,  Mista Katmwan Dungse ya bayyana cewa irin shirin da jihar ta yin na samar da ingantattun kayan wasa da filayen wasa abin burgewa ne, don haka yana sa ran jihar za ta iya karbar bakuncin wannan wasa a 2022.

Wuraren da suka duba sun hada da Filin Wasa na MKO Abiola da Abeokuta Sport Club da Alake Sports Center da Ijeja da June 12 Cultural Center Kuton da Abeokuta Grammar School da Gateway International Stadium Shagamu da Sansanin Horar da Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC)da kuma Filin-wasa na Dipo Dina da ke Ijebu-Ode.