✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Odinga ya yi kiran kaurace wa zaben Kenya

  Jagoran Jam’iyyar adawa a Kenya, Raila Odinga ya yi kira ga magoya baya da su kauracewa zaben shugaban kasar da ya gudana jiya Alhamis,…

 

Jagoran Jam’iyyar adawa a Kenya, Raila Odinga ya yi kira ga magoya baya da su kauracewa zaben shugaban kasar da ya gudana jiya Alhamis, a cewarsa babu abinda ya sauya a tsarin hukumar kan gudanar da sahihiyar zabe.

 

Dubban magoya bayan Raila Odinga daga lungu da sakon kasar sun amsa kiran gwanin nasu da ya janye daga takarar shugabancin kasar bayan fitar da sanarwar sake zaben da aka soke bisa zargin cewa an tafka kura-kurai da suka sabawa doka.

 

Mahunkunta a kasar sun ce zaben shugaban kasar yana gudana kamar yadda aka tsara duk kuwa da takaddamar da ke tattare da zaben da a sakamakon farko ya bai wa shugaba mai ci Uhurru Kenyatta nasara. Babban kotun kolin kasar ta sanar cewa an gagara saurarar kara da aka shigar a gaban kotun na neman dage zaben, alkalin kotun, Dabid Maraga ya ce su biyu kacal suka halarci zaman ba tare da ya yi karin bayani kan dalilan da suka hana sauran halartar zaman ba.

 

daruruwan mutane wadanda akasarinsu mata ne sun gudanar da gangami don yin kira ga sauran al’ummar kasar da su rungumi zaman lafiya su kuma guji duk wani abu da zai haifar da rikici a wannan yanayi da kasar ta samun kanta ciki.