✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obaseki ya kai wa Buhari ziyara

A ranar Juma’a Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke birnin Abuja. Gwamnan bayan ganawarsa da Shugaban…

A ranar Juma’a Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke birnin Abuja.

Gwamnan bayan ganawarsa da Shugaban Kasar, ya shaida wa manema labarai cewa butulci ne a gare shi ya koma jam’iyyar APC bayan ya ci zabe a PDP.

Obaseki na jam’iyyar PDP, shi ne Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar ya lashe zaben jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar bayan ya lallasa babban abokin hamayyarsa, Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC.

Karo na biyu ke nan da Obaseki ya tika Ize-Iyamu da kasa, bayan irin hakan ta kasance a 2016, a lokacin yana APC, Ize-Iyamu kuma na PDP.

Ya sauya sheka daga APC zuwa PDP bayan APC ta hana shi takara a zaben fidda gwani.

Ana yi ta rade-radin cewa zai iya komawa APC bayan ya lashe zaben a PDP.

Sai dai Gwamna bayan ganawarsa da shugaban kasa tare da mataimakinsa, Philip Shuaibu, ya ce butulci ne a gare shi ya koma jam’iyyar APC bayan samun nasara a PDP.