A ranar Juma’a Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke birnin Abuja.
Gwamnan bayan ganawarsa da Shugaban Kasar, ya shaida wa manema labarai cewa butulci ne a gare shi ya koma jam’iyyar APC bayan ya ci zabe a PDP.
- Gwamna Obaseki ya lashe zaben gwamnan Edo
- Obaseki ya karbi shaidar cin zaben Edo
- Abin da Kwankwaso ya ce kan nasarar Obaseki a zaben Edo
Obaseki na jam’iyyar PDP, shi ne Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar ya lashe zaben jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar bayan ya lallasa babban abokin hamayyarsa, Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC.
Karo na biyu ke nan da Obaseki ya tika Ize-Iyamu da kasa, bayan irin hakan ta kasance a 2016, a lokacin yana APC, Ize-Iyamu kuma na PDP.
Ya sauya sheka daga APC zuwa PDP bayan APC ta hana shi takara a zaben fidda gwani.
Ana yi ta rade-radin cewa zai iya komawa APC bayan ya lashe zaben a PDP.
Sai dai Gwamna bayan ganawarsa da shugaban kasa tare da mataimakinsa, Philip Shuaibu, ya ce butulci ne a gare shi ya koma jam’iyyar APC bayan samun nasara a PDP.