✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Obasanjo ya yi direban Keke Napep na yini daya

A ranar Asabar din nan ce tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi direban babur mai kafa uku wanda ake kira Keke Napep a…

A ranar Asabar din nan ce tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi direban babur mai kafa uku wanda ake kira Keke Napep a Jihar Ogun.

Daruruwan mutane maza da mata ne suka sha mamaki yayin da suka fito titi kallon tsohon shugaban kasar yana shawagin neman fasinja a babur din mai kafa uku a titunan Abeokuta, babban birnin jihar.

Wani mai daukar hoto dan Najeriya mazaunin Landan daga yankin Ijebu na Jihar Ogun, Daniel Olusanya ne ya wallafa hotunan tsohon shugaban kasa a shafinsa na Facebook.

Hotunan sun nuna yadda tsohon shugaban kasar rike da kan babur din mai kafa uku yana tuki tare da daukar fasinjoji a kan hanyar da ta taso daga gidansa zuwa Unguwar Kuto a garin na Abeokuta.

Wannan lamari dai ya burge daruruwan mutane a kan hanyoyin da Obasanjo ya ratsa yana tuka babur din mai kafa uku.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, tsohon shugaban kasar wanda a watan jiya na Yuni ya bayar da kyautar babura masu kafa uku ga mutane 85 a garin Abeokuta, ta ce ya yi hakan ne domin nuna murnarsa ga zagayowar watan wanda a cikinsa ne ya cika shekaru 85 da haihuwa.