✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obafemi ya sayi motar Naira Miliyan 100

Shahararren dan kwallon Super Eagles da yanzu haka yake buga kwallo a kasar Sin Obafemi Martins ya sayi sabuwar mota kirar Bently da aka kiyasta…

Shahararren dan kwallon Super Eagles da yanzu haka yake buga kwallo a kasar Sin Obafemi Martins ya sayi sabuwar mota kirar Bently da aka kiyasta kudinta a kan Naira Miliyan 100. dan kwallon ne da kansa ya sanar da haka a shafin sadarwarsa ta Instagram a ranar Talatar da ta gabata.

dan kwallon da yanzu haka ya cika shekara 33 yana wasa ne a wani kulob mai suna Shanghai Shenhua da ke kasar Sin.  A kwanakin baya ne ya taimaki kulob din wajen lashe gasar cin kofin kalubale na Sin.

An ce dan kwallon ya bar Najeriya ne tun yana dan shekara 16 inda ya koma kasar Italiya.  A shekarar 2002 ce ya fara buga wa kulob din manya na Inter Milan da ke Italiya inda daga nan tauraruwarsa ta rika daukaka inda ya yi wasa a kulob da dama ciki har da na Newcastle da ke Ingila kafin ya koma Chaina don ci gaba da yin kwallo.

Obafemi ya nuna babban burinsa shi ne ya mallaki irin wannan mota, don haka yanzu tamkar mafarkin da yake yi ya zama gaskiya kenan.

Martins yana daga cikin ’yan kwallon da ke hankoron halartar gasar cin kofin duniya a Rasha idan kocin Super Eagles ya gayyace shi.