Nura Al-Amin matashi ne da larurar nakasa ta shanye wa kafa, sai dai hakan bai hana shi yin sana’a ba. Ya bayyana wa Aminiya dalilin shigarsa sana’ar yin takalma da yadda yake gudanar da ita tare da yaran aikinsa 18, kamar haka:
Aminiya: Mene ne tarihinka a takaice?
Sunana Nura Al-Amin, iyayena ’yan asalin garin Minna da ke Jihar Neja ne, sai dai a garin Madalla aka haife ni. Ina da kamar shekara 23 da haihuwa. Na yi karatun firamare, na fara ne a shekarar 2003 na kuma kammala a shekarar 2009, sai dai ban samu damar zuwa gaba ba saboda kalubalen rashin kudi.
Aminiya: Yaushe ka fara wannan sana’a?
Na je wajen wanda yake yin sana’ar ne wato maigidana ke nan a kan ya yi mini takalman da za su dace da kafafuna kasancewar ina da larura ta shanyewar kafa, to a nan ne sai na ji ina sha’awar sana’ar, bayan na bayyana masa hakan sai ya karfafa mini gwiwa. Haka nan na fara zuwa wajen aikin har na koya, na kuma shekara kamar uku muna tare bayan nan ne sai ya sallame ni ya kuma kama mini wannan shago da nake aiki bayan ya hada mini kayan aiki. A yanzu ina aiki a wajen nan kamar shekara shida ke nan.
Aminiya: Kamar wadanne nau’o’in takalma ne kake kerawa?
Akwai takalma samfurin silifas da masu igiya da ake yi wa lakabi da Easy Wear na maza da mata, ga sunan dai kamar yadda ka gan su, sai dai ba na yin sawu ciki. Shi silifas din ina sayar da shi a kan Naira 800, farashinsa ya dara na kasuwa ne saboda ingancinsa da kuma tudu da yake da shi, yakan kuma jima bai lalace ba. Su kuma masu igiyar mukan sayar da su a kan Naira dubu daya ne, sai kuma takalman mata da muke sayarwa Naira dari 600.
Aminiya: Yaya batun kayan aiki?
Kayan aiki ya rabu kashi biyu ne. Akwai na dindindin, akwai kuma na samowa yau da kullum. Kamar na dindindin akwai janaretan samar da wutar lantarki, da keken dinki da na’urar daidaita kasan takalmi bayan an yanka, sai kuma almakashi. Ana yau da kullum kuma wanda a garin Suleja muke saya, sun hada da kasan takalmi wato sole da fatar leda da kuma gam, akwai kuma kirtani ko kananan kusa da a wani zubin muke amfani da su a wasu nau’o’in takalman da sauransu.
Aminiya: Kamar mutum nawa suke koyon sana’ar a karkashinka?
Ina tare da kamar mutum 18 da ke karkashina. Akwai wadansu da suka fara yin kananan ayyuka kamar yanka kasan takalma bayan an zana musu, wadansu kuma sun ma iya zanawa, sai kuma wadanda suka yi nisa kusan sun iya yin komai.
Aminiya: Takalma nawa kuke hadawa a wuni guda?
A wuni daya muna yin takalma kamar 25 zuwa 30 wadanda nau’o’i ne daban-daban, kuma kamar mutum biyar ne ke sa hannunsu a aikin. Ni na fi yin bangaren hada saman da saitawa da kuma gogewa, su kuma yarana sun fi yin bangaren yankawa ne da kuma zanawa.
Aminiya: Wane ci gaba wannan sana’ar ta kawo maka?
A gaskiya na samu ci gaba sosai a wannan sana’a daga ciki akwai rike gidanmu da kuma kannena da ke makaranta, baya ga biyan bukatun kaina, sannan kamar yadda na gaya maka akwai wadanda ke karkashina da ke koyon sana’ar, wannan ba karamin abin farin ciki ba ne.
Aminiya: Akwai wani kalubale da kake fuskanta?
kalubalen wannan sana’a a yanzu shi ne tashin farashin kayan aiki da muke amfani da su, sannan idan muka yi kari a kan farashin na baya, sai ka ga ciniki na yin nauyi, ga kuma matsalar rike kudi a wani zubin daga bangaren abokan hulda idan sun amshi kaya ba tare da biyan gaba dayan kudinsu ba.
Aminiya: Kana da wani buri?
Babban burina shi ne in kara fadada sana’ar ta hanyar yin wasu abubuwa da ba ma yi a yanzu bayan samun kayan aiki, sai kuma ci gaba da koya wa wadansu don rike kansu da kuma jama’arsu.