✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NSE ta bukaci hadin gwiwar yaki da Injiniyoyin bogi a Najeriya

Kungiyar Injiniyoyi ta kasa (NSE) reshen Jihar Edo, ta yi kira ga mambobin kungiyarta da su hada hannu wurin yaki da Injiniyoyin bogi a fannin…

Kungiyar Injiniyoyi ta kasa (NSE) reshen Jihar Edo, ta yi kira ga mambobin kungiyarta da su hada hannu wurin yaki da Injiniyoyin bogi a fannin nasu da suke da kwarewa a kai a fadin Jihar da Najeriya baki daya.

Shugaban Kungiyar na Jihar Edo, Injiniya Omoregie Ehigie ne ya yi wannan kiran a birnin Benin a karshen mako yayin da ya ke rantsar da wani kwamitin kwararru (ESTC) da kwamitin sa ido kan ayyukan Injiniyoyi a Jihar Edo.

Ya bayyana cewa an yi asarar gine-ginen mutane da dama sakamakon ire-ren ayyukan Injiniyoyin bogi da suka yi wa harkokinsu shigar sojan gona.

“Ta hanyar kaddamar da wannan kwamitoci ne, za a kawo karshen Injiniyoyin bogi.

“Na kosa da mutanen da basu da kowane irin horo ko kwarewa amma suke kiran kansu da suna Injiniyoyi; Injiniyanci lamari ne mai matukar muhimmanci da yake bukatar aiki a aikace tamkar na likitacin” in ji shi.

Omoregie ya yaba wa Majalisar dake kula da ayyukan Injiniyoyi ta Najeriya (COREN), sakamakon rawar da take taka wa na ganin an samar da sahihan Injiniyoyi masu kwazo da hazaka wadanda suka cika sharudan zama Injiniyoyi a ko ina a fadin duniya.

“Ina amfani da wannan dama na sanarwa jama’a cewa abubuwa ba za su tafi kamar yadda muke tafiyar da su ba. Injiniyoyinmu a shirye suke wurin ganin al’amura sun tafi ta kowace fuska don ganin sun tabbatar da ba wa jama’ar Jihar Edo kariya ta kowace fuska kamar yadda yace.

Shugaban Majalisar ta COREN, Mista Ali Rabiu, ya yi kira ga dukkan Injiniyoyi da su tabbatar suna dauke da shaidar kwarewa ta COREN kamar yadda yake a matsayin sharadi na farko kan kowane mai aikin Injiniya a Najeriya.