Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta yi Allah-wadai da kisan wasu matafiya Musulmai 25 da aka yi a Jos, a kan hanyarsu ta koma wa Jihar Ondo daga Bauchi ranar Asabar.
Majalisar, wacce ke karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta sanr da haka ne a cikin wata sanarwa da Daraktanta na Mulki, Akitek Zubairu ya fitar ranar Lahadi ya yi kira ga Musulmi das u kwantar da hankulansu kuma kada su dauki doka a hannunsu.
“Majalisarmu na jaddada cewa babu wani rai da ya kamata a dauka saboda addininsa ko kabilarsa. Za mu ci gaba da zuba ido a binciken da ake yi mu tabbatar an yi adalci.
“Kazalika, yayin da ake ci gaba da yunkurin nemo ragowar mutum takwas din da har yanzu ba a gansu ba, muna kira ga jami’an tsaro da su tabbatar sun zakulo masu hannu a cikin lamarin tare da hukunta su,” inji sanarwar.
A wani labarin makamancin wannan, kungiyar nan mai rajin kare muradun Musulmai ta MURIC ita ma ta yi kira da a gaggauta kamawa tare da hukunta duk masu hannu a kisan.
A cikin wata sanarwa da Daraktan kungiyar na kasa, Ishaq Akintola ya fitar, MURIC ta ce, “Muna Allah-wadai da kalaman Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato da takwaransa Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo wadanda suka yi ikirarin cewa wai kisan kuskure ne.
“Wannan hanzarin da suka yi saurin bayarwa na nuna alamar suna da masaniya a kan kisan. Abin kunya ne yadda Gwamna Akeredolu zai nesanta kansa da ’yan Jiharsa, saboda kawai Musulmai ne.
“Shi kuwa Gwamnan Lalong ba yadda za mu yi mu yarda da shi saboda yana kokarin yin rufa-rufa ne saboda mutanensa ne suka aikata hakan, da ya samu dama zai shashantar da maganar, saboda ya sha yin hakan a baya.
“Har yanzu ba mu manta da kisan Janar Alkali ba, musamman yadda aka yi yunkurin rufe maganar, yadda aka gano gawarwakin mutane a kududdufi da yadda Gwamnan ya garzaya shalkwatar sojoji ya nema musu afuwa.
“Mun dauka cewa wutar rikici ta lafa a Jos, amma wannan kisan kiyashin na ranar Asabar kan Musulmai masu yawa ya bayyana munafuncin da Gwamnan da mutanensa ’yan ta’adda suke aikata wa.
“Ban da ’yan sanda da sojoji sun kawo dauki, da tuni an kashe dukkan musulman da suke cikin motocin guda biyar kuma a jefa gawarwakinsu cikin kududdufai kamar yadda aka saba,”inji MURIC.