✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NRC ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

NRC na neman afuwar al’ummar da wannan tsaiko na jigilar jirgin zai shafa.

Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna sakamakon gocewa daga layin dogo da wani jirgi ya yi ranar Juma’a.

Daraktan NRC Niyi Alli ne ya bayyana hakan, yana mai neman afuwar fasinjojin jirgin da wannan tsaiko zai shafa.

“Hukumar gudanarwar NRC na bakin cikin sanar da fasinjojinta na jirgi mai lamba AK3 da na KA4 cewa mun dakatar da jigila dalilin sauka daga kan layin dogo da daya daga cikin jiragenmu ya yi ranar 27 ga Janairun 2023.

“Da Taimakon Ubangiji ba a samu wanda ya yi rauni ba ko daya, sai dai duk da haka muna neman afuwar al’ummar da wannan tsaiko na jigilar jirgin zai shafa.

“Tuni tawagar NRC ta fara kokarin gyara matsalar,” in ji Alli.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan dawowa jigila da jirgin ya yi, wanda aka dakatar sakamakon sace fasinjojin da ’yan bindiga suka yi a watan Maris na bara.