✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu sanar da ranar da jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki ba – NRC

Hukumar ta ce labarin ba daga wajenta ya fito ba

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta musanta labarin da ke yawo cewa za ta dawo da zirga-zirgar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna ranar 24 ga watan Nuwamban 2022.

Rade-radin na cewa hukumar za ta dawo da sufurin jirgin a wannan ranar 24 ba shi da tushe ballantana makama.

Shugaban hukumar Fidet Okhira ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa labarin da ake yadawa karya ne, a kuma a yi watsi da shi.

“Ina so in sanar da jama’a cewa, wannan labari da ake yadawa karya ne, saboda babu wata takamaiman rana da aka sa na dawo da zirga-zirgar jirgin kasa,” inji  shugaban hukumar.

Sai dai kuma ya ce, gaskiya ne Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, ya sanar da cewa za a dawo da zirga-zirgar jirgin kasar a cikin watan Nuwamba, kuma ana duk mai yiwuwa na ganin hakan ta tabbata.

Sannan shugaban ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar na tabbatar da tsaro ga rayuka da kuma dukiyoyin jama’a musamman fasinjojin jirgin.

Bayan sakin sauran fasinjojin da  suka rage a hannun ’yan ta’adda  da suka kai hari kan jirgin kasar da ke zirga-zirga kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, gwamnati ta sanar cewa zai dawo da sufuri a cikin watan Nuwamba.

NAN