Alhaji Kamilu Sa’idu Sigau, wani babban manomin masara ne, a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna. A tattaunawa da wakilinmu, ya yi bayani kan mawuyacin halin da manoman masara suke ciki, bisa yadda kakar bana tazo masu, na rashin yawan masarar da suka samu a gonakinsu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
A matsayinka na babban manomin masara, yaya ka ga yadda kakar masara ta kasance a bara?
Gaskiya mu manoman masara, muna yi wa Allah godiya kan yadda kakar bana ta kasance.
Tun da mun yi aikin noma lafiya, kuma mun gama lafiya, don haka muna yi wa Allah godiya.
Yaya ka ga amfanin gonar da manoman masara suka samu a bana?
Gaskiya a daminar da ta gabata, an samu akasi a noman masara, sabanin shekarun baya. Kusan zan ce a sama da shekara 20 ban taba ganin daminar da aka samu karancin amfanin gona musamman masara, kamar daminar da ta gabata ba.
Domin a bana za ka ga mutumin da yake samun buhu 100 duk shekara, a bana abin da ya samu bai wuce buhu 40 ba.
Wani kuma za ka ga duk shekara yana samun buhu 10,000, amma a bana abin da ya samu buhu 1,000 ko buhu 1,500. Kuma ya yi wa gonar komai na aiki kamar yadda ya saba. Gonar da aka kashe wa kudi Naira miliyan daya a bara, a bana an kashe mata Naira miliyan biyu.
A bara an sayar da buhun masara Naira 23,000, amma a bana an zo ana sayar da buhun masara Naira 17,000. Bayan kudin da aka kashe wajen noman masarar a bana ya ninka na bara. Kuma ga matsalar karancin amfanin gona da aka samu. Gaskiya bana manoman masara suna cikin mawuyacin hali.
Me kake ganin ya kawo mawuyacin halin da suka shiga?
Gaskiya wannan al’amari wani abu ne daga Allah. Domin a bana an samu ruwan sama, amma ruwan ya zo ne bayan masara ta riga ta nuna. Wannan abu wani al’amari ne daga Allah.
Ganin mawuyacin halin da ka ce manoman masara sun shiga, yaya kake ganin noman masara zai kasance a damina mai zuwa?
Gaskiya a fahimtata da noma a matsayina na manomi wanda na taso a cikinsa, na kuna gada daga iyaye da kakanni, za a sha wahala wajen noman masara a damina mai zuwa. Domin a yanzu haka, idan manomi yana da masara buhu 100, zai yi wahala ta kara noma masa wata masarar buhu 100.
A bazarar bara, ana sayar da litar man gas da ake sa wa taraktar noma a kan Naira 200 amma a bana mun sayi litar man gas a kan Naira 800 zuwa 900. Kuma a kakar bara, mun sayi takin zamani a kan Naira 8000 zuwa 10,000, amma yanzu ana sayar da buhun takin Yuriya a kan Naira 24,000.
Yanzu idan manomi yana son ya sayi taki buhu daya, sai ya sayar da buhun masara biyu.
Wadanne hanyoyi kake ganin za abi a warware matsalar da manoman masara suka shiga?
Gaskiya mai gyara wannan al’amari sai dai Allah. Domin wannan al’amari ya fi karfin gwamnati, sai dai Allah kadai. Babu wani tallafin da gwamnati za ta bai wa manoma da zai magance wannan al’amari. Sai dai Allah kadai.
Saboda abin da yake faruwa yawancin kananan manoma, sun riga sun karye ta dalilin karbar bashin noman nan na Anko Borowas. A da, kafin wannan bashi ya zo, za ka ga manomi yana noma masara buhu 20 zuwa 30, yana gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali da iyalansa.
Amma da aka zo da wannan bashi, sai wasu kananan manoman suka karar da masara da suke nomawa a wasu safgogi, wasu suka yi aure, wasu suka yi gini da sauransu. Yanzu kananan manoma sun dawo suna rayuwa a kan doron bashi.
Kuma a bana, sai aka wayi gari manomin da ya je ya karbi bashi na babbar gona ko na Aped, ana neman buhun masara 20, yana tunanin zai samu buhun masara 60 a gonarsa, sai ya wayi gari gonar baki daya ba ta wuce buhun masara 20 ba.
Kuma ga shi kamfani suna jiran ya kawo masu masara buhu 20. Ka ga ba zai iya biyan bashin da ake bin sa ba, balle ya ajiye wadda zai ci. Halin da manoman suke ciki ke nan a yanzu. Kuma har yanzu gwamnati ba ta san wannan hali da manoma suka shiga ba.
Abin da ya sa na ce haka shi ne, amfanin gona ne kadai za ka saya a farashin shekara 10, ka zo ka samu har yanzu yana nan a wannan farashi. Amma duk da haka, gwamnatin nan ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta fito da tsari mai kyau kan bunkasa harkokin noma.
Don haka babu abin da za mu ce mata, sai dai mu yi mata fatar alheri. Domin a Najeriya ba a taba samun gwamnatin da ta taimaki manoma, suka samu arziki kamar wannan gwamnati ba. A wannan yanki namu, kashi 50 na gine-ginen da aka yi a garuruwa da kauyuka an yi su ne da kudaden noma.
Manoman wannan yanki sun sayi abubuwan hawa, kamar motoci da babura, duk da kudin da suke samu daga noma.
Tunda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau kan mulki, shekaru 8 da suka gabata, wannan shekara ce kadai manoma suka samu matsala ta rashin cin ribar amfanin gonar da suka noma. Kuma ita ma abin da ya kawo haka, shi ne rashin samun amfanin gona da yawa.
Don haka, muna kira ga gwamnati ta ci gaba tsarin da ta dauko na sayen amfanin gona. Wato su ci gaba da saye da daraja suna sayar wa kamfanoni. Domin manomi ya samu kudin da zai sayi taki da maganin feshi, ya samu ya sake noma masara a damina mai zuwa.
Saboda yanzu ko manomi ya sayar da buhun masara a kan Naira 30,000 da yawa kudinsu ba zai fita ba.