✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Noman kashu zai samar da ayyuka 500,000 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kudaden shiga na kusan Naira biliyan 25 a duk sherara a bangaren noman kashu wanda zai samar…

Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kudaden shiga na kusan Naira biliyan 25 a duk sherara a bangaren noman kashu wanda zai samar da ayyukan yi ga mutum 500,000.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Kasa, Dokta Abdulkadir Mu’azu, shi ne ya bayyana haka a taron manoman kashu da masu ruwa da tsaki a harkar nomansa, wanda Cibiyar Nazari da Bincike kan Harkokin Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta gudanar a karshen mako.

Babban Sakataren ya ce, Gwamnatin Tarayya tana da wani kuduri da take burin cikawa a 2021 zuwa 2024.

Sakataren wanda ya samu wakilcin Mataimakin Darakta a Sashen Harkokin Noma na ma’aikatar, Bernard Chukwuemeka, ya ce ma’aikatar ta kammala dukkannin shirye-shiryenta na samar da iri don noman kashu.

Darakta a Cibiyar, Farfesa Mohammed Ishiyaku, ya ce cibiyar ta gudanar da bincike sama da kala 50 kan iri daban-daban na kashu, ya kuma yi alkawarin samar da karin wasu irin na daban akalla guda14.

Ya ce nan da shekarar 2021, cibiyar za ta kaddamar da sabbin nau’ika uku na irin kashu.