Haka kananan manoma gwamnati ta rika hada makwaftan gonaki guda dari (100) ko fiye bacin an bai wa kowannensu taswirar girman gonarsa, a yi kiyasin irin da za’a shuka a gurin, tare da abincin dabbobi, gwamnati ta dauki nauyin bayar da irin bashi, a yi musu noma da feshi bashi, a ba su taki bashi, su biya ma’aikata, sai an yi girbi su biya gwamnati da amfanin gonar ko LBA’s su saye, a biya gwamnatin da kudi. Ribar a raba dai-dai da girman gonar kowa. Wannan ita ce hanya mafi sauki da gwamnati zata sani idan an sami fari, su dauki matakin taimako ga wadanda abin ya shafa. Ta haka ne kowa zai samu aikin yi wanda zai rike kansa da iyalansa ba tare da ya roki kowa ba, musamman tunda mafiya yawan shugabannin da muke da su, ‘yan kauye ne, ‘ya’yan masu yin irin wadannan sana’oi. Sai su samar da ababen more rayuwa a kowanne kauye da wuraren sana’oin da suke yi, kamar makarantu da asibitoci da ofisoshin ‘yan sanda da hanyoyi da lantarki da ruwan famfo da kasuwannin na zamani, da tashoshin mota manya da kanana na zamani. Kamar yadda Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya kirkiro Greater Kano Planning Authority da ake kira KNUPDA yanzu. Yadda za a kara fadin Birnin Kano da kimanin kilo-mita ashirin-ashirin (24-24). Gabas da Yamma da Kudu da Arewa. Idan aka gina manyan tashoshi da (Ware-Houses) a kowanne bangare, duk wasu manyan motoci anan za su sauke kayan da suka dauko, kananan motoci su yi jigilar kaiwa cikin Birni. Ban da na fetur da gas da kananzir kafin a dawo da jiragen kasa. Ta haka ne za a tabbatarewa da cikakken tsaro da rage kwararowar mutanen kauye zuwa birni, suna aikata abuwan da da ba su kamata ba. A rage lalacewar titunan. Wajibi ne mu komo da tsarin ciyar da kasa gaba na shekaru biyar-biyar (FIbE YEAR DEbELOPMENT PLANNING).
Injinan da ya kamata Gwamnati ta shigo mana da su, sun hada da wadanda za a rika sarrafa dorawa, tun daga makuba da gaskami da kunun zaranya da daddawa harzuwa itacen ta. Haka Zogale da aka ce tana yin magani (99) da darbejiya da sauran bishiyoyi da tsirrai da Allah ya azurtamu da su, bacin ‘ya’yan itatuwa da kayan miya; Tumatir da tattasai da albasa da barkono da sauransu. Idan aka kafa masana’antun da za su sarrafa duk wadannan kowa zai samu aikin yi ya azurta gwargwadon arzikin da Allah ya yi masa, zaman lafiya tsakanin al’umma zai inganta. Sai dai Gwamnti ta dogara da mutane, ba mutane su rika dogara da Gwamnati ba.
Sai Maganar Adalci:
Masu mulki da Hukumar Shari’a da jami’an tsaro su rika aiwatar da hukunci a kan kowa daidai da laifin da kowa ya yi babu tsimbure. Shi ne kubutarsu a gurin Allah da fushin Talakawa, musamman wadanda aka zalunta. A magance duk wasu ‘yan damfara, aljanun karya, matsafa da ‘yan tsubbu da fajirai masu jawo annoba ga al’umma baki-daya, musamman annobar mutuwa.
Duk kasar da ba ta iya ciyar da kanta, ba ta da ‘yanci balle zaman lafiya. Idan muka koma kan addini, babu addinin da ya yarda a yi zulunci ko sata ko tsafi ko fajirci. Addinin Musulunci ya yi umarni a rika fitar da Zakkah ana bai wa mabukata. Da Hukuncin da za a yi wa duk wanda ya aikata kowane irin laifi, shi ya sa aka halatta kotuna da alkalai da jami’a tsaro da Kurkuku, da yin haddi a kan masu aikata zina da kisa da sata da makamantansu. Duk abin da aka kasa hanawa, masu hanawa ne suke yi. Idan ma wasu masu mulki sun bijire akwai ranar haduwa da Allah. Wanda ya haramta wa kansa yin zulunci ya yi umarni kada kowa ya yi zalunci. Annabi (S.A.W) ya ce: “matukar al’umma suna aikata zina – Allah zai saukar musu da annobar mutuwa, idan suna tauye ma’auni – za’a kwashe musu albarkar kasa, idan suna karya alkawari – makiyansu zasu rinjaye su , idan basa fitar da Zakkah – za’a yi fari ko yunwa, idan ba sa yin Sharia da Littafin Allah Mai Tsarki – za su shiga dimuwa. Shiyasa ya ce idan muka ga barna mu hana ta da hannunmu, idan ba mu da iko mu hana da baki, idan ba mu da iko sai mu ki abin a zuci (wannan shi ne mafi raunin imani)”.
Ina amfanin badi ba rai? Ka yi mulki, ka yi sata, ka rasa inda za ka boye, kana tsoron ka fito da su kowa ya sani kai barawo ne, ga bukatu sun sameka, ka rasa yadda za ka yi, ga talakawa suna cikin kunci, fatara da yunwa da cutuka. Ga koshi ga kwanan yunwa. Nan gaba za a yi rigima, fura da nono da zuma, ga ta gaban mai hadama, Mayunwaci ne bai sha ba.
Alh. Abdulkarim Daiyabu, Tsohon Shugaban kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu Da Ma’adanai da Aiyukan Gona ta Jihar Kano (KACCIMA) Shugaban Rundunar Adalci Ta Nigeria (MOJIN) 08060116666, 08023106666.
Noma da kiwo da sana’o’in hannu (2)
Haka kananan manoma gwamnati ta rika hada makwaftan gonaki guda dari (100) ko fiye bacin an bai wa kowannensu taswirar girman gonarsa, a yi kiyasin…