✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa China da Japan

Kamfanin Mai Na Najeriya (NNPCL) ya ce ya fitar da gas zuwa ƙasashen Japan da China domin sayarwa. Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ambato Shugaban…

Kamfanin Mai Na Najeriya (NNPCL) ya ce ya fitar da gas zuwa ƙasashen Japan da China domin sayarwa.

Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ambato Shugaban Hukumar tace mai na NNPC, Segun Dapo, na cewa hakan na daga shirye-shiryen kamfanin na kasancewa mai samar da nagartaccen makamashi a kasuwannin duniya.

Dapo ya ce bangarensa ya samu gagarumin hadin kai daga bagarorin kamfanin NNPC na gas da kuma na sufurin jiragen ruwa.

A sakamakon haka, jirgin farko dauke da gas din sayarwa ya bar Najeriya zuwa Japan a ranar 27 ga Juni, 2024.

“A shekarar 2021 NNPC ya fara harkar kasuwancin gas kuma kawo yanzu ya fitar da jirager ruwa sama da guda 20 na gas zuwa yankunan Asiya da turai.

“Hakan zai ba kamfanin damar fadada harkokinsa domin samun kaso mai yawa a bangaren ta yadda zai kara shahara da harkar iskar gas,” in ji Dapo.

Nan da watan Nuwamba, ana sa ran NNPC zai kai jirage sama da biyu na gas zuwa kasuwannin kasahen Asiya, har da kari kafin karshen shekara. (NAN)

Tsarin kasuwancin ya kunshi masu kaya su kai tashoshin jiragen ruwan da ake kebe musu domin kayan da ake bukata a kasunannin duniya.

Sai dai mai kayan ne ke daukar alhalin inshorar kayansa har zuwa lokacin da za su isa inda ake bukatarsu.