✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPC zai ci gaba da neman mai a Tafkin Chadi

Kamfanin Mai na kasa wato NNPC ya ce zai ci gaba da binciken neman man fetur Tafkin Chadi saboda yadda ake ci gaba da samun…

Kamfanin Mai na kasa wato NNPC ya ce zai ci gaba da binciken neman man fetur Tafkin Chadi saboda yadda ake ci gaba da samun kwanciyar hankali a yankin Arewa-maso-Gabas.

Shugaban Kamfani Dokta Joseph T. Dawha ne ya bayyana hakan a lokacin taron shekara-shekara karo na 21 a Abuja.
Kamfanin ya dakatar da binciken ne a yankin bayan da aka kwashe shekaru ba tare da samun nasara ba, bayann an hake rijiyoyi 23.
Har ila yau, yunkurin ci gaba da aikin ya ci tura saboda matsalolin tsaro. Kodayake, ba kamfanin NNPC ba ne kawai yake aikin neman man a yankin, kwai kamfanin Shell da Chebron da kuma Elf.
Kodayake, Dokta Dawha ya ce: “kwarya-kwaryan binciken da aka gudanr ya nuna cewa akwai alamun nasara kuma wannan ya sa za a koma yankin domin ci gaba da binciken. Ya dace mu yaba wa jami’an tsaro bisa nasarar da suke ci gaba da samu a yakin da suke yi da masu tada kayar baya.”