Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana bakawai ta kawo karshen wahalar man fetur da ta takardun kudi a fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, ne ya sanar da lokacin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar kungiyar ta kasa da ke Abuja, kan matsayin taron kungiyar ranar Litinin.
- ’Yan ci-rani 22 sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Madagascar
- Isra’ila ta saki Bafalasdine bayan ya shafe shekara 17 a daure
Ya ce matukar ba a iya magance matsalolin ba nan da cikar wa’adin, za su tsunduma yajin aiki.
Shugaban kungiyar wanda ya koka da irin mawuyacin halin da wahalhalun suka jefa ’yan Najeriya, musamman ma ma’aikata ya sa kungiyar ba zai yiwu ta ci gaba da yin shiru ba.
“Da farko dai za ku lura da yadda ’yan Najeriya da dama musamman ma’aikata suke kalubalantar yadda suke shan wahala kafin samu kudadensu daga bankuna. Haka ma matsalar man fetur, inda a wasu wuraren lita yake kai wa har N300, ko ma sama da haka.
“Saboda haka, a kan matsalar karancin kudi, muna ba Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran bankuna wa’adin kwana bakwai su magance ta.
“Muddin kuma suka gaza yin haka, za mu bukaci daukacin ma’aikata su kaurace wa wuraren ayyukansu, tun da dai ba su da kudin zuwa wajen aiki.
“Sannan yin sayayya ma a wajen ’yan kasuwa yana da matukar wahala, saboda wasu daga cikinsu ba su da asusun ajiyar bankuna,” in ji shi.
Shugaban na NLC ya kuma zargi wasu Gwamnoni da yin katsa-landan a cikin harkokin kungiyar, ta hanyar tursasawa a sanya mutanensu a matsayin Shugabanni a Jihohi.