✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NLC da gwamnati za su sa labule kan cire tallafin mai

Shugaba NLC ya ce bai kamata a cire tallafin ba tare da ana samar da man ba, daga karshe a bar  dillalan mai suna tatsar…

Kungiar Kwadago za ta tattauna da Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba kan dambarwar cire tallafin mai da ya haddasa tsadarsa da kuma dogayen layi.

Shugaban NLC Joe Ajaero,  ya ce ya kamata Shugaba Tinubu ya fara duba halin da ’yan Najeriya ke ciki, ya kuma samar da abubuwan da za su rage radadin cire tallafin da ga jama’ar kasa kafin ya yanke shawarar cire tallafin.

Matakan, a cewarsa, sun hada da gyara matatun man gwamnati hudu da kuma samar da tsarin jigilar ma’aikata kyauta da sauransu.

Amma ya ce: “Da alama gwamnati na son a tattaunawa, kuma sun sanya karfe 2 na ranar Laraba a matsayin lokacin da za mu fara tattaunawa.

“Akwai bukatar tattauna abubuwa da dama, saboda bai kamata a cire tallafin ba tare da ana samar da man ba, daga karshe a bar  mu a hannun dillalan mai suna azabtar da mu domin su ci riba.

“Maganar shugaban kasa na cire tallafin daidai yake da doka, amma ya kamata a yi dokar da za a iya dabbakawa; sannan mutanen da suka yi dokar, su ne za su yi wannan,” in ji Ajaero yana mai bukatar Shugaba Tinubu ya sauya shawara kan cire tallafin.

Ya ce, “Mene ne a bin jin dadi a cire tallafin amma mutane su shiga cikin wahala? Ai abin da ya fi dacewa shi ne shugabanni su dubi yadda za a rage wa jama’a wahalar da suke ciki a halin yanzu.”