✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela 300 dauke da kayan abinci sun shiga Nijar daga Burkina Faso

Manyan motoci 300 dauke da kayan abinci daga gwamnatin sojin Burkina Faso sun isa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar

Jerin gwanon manyan motoci 300 makare da kayan tallafi ga sabuwar gwamnatanin sojin Nijar daga kasar Burkina Faso sun isa Yamai, babban birnin kasar.

Gwamnatin sojin Burnkina Faso ta tura wa takwararta ta Nijar tallafin kayan abinci da sauransu ne domin rage mata radadin takunkumin karya tattalin arziki da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan da ya gabata ne kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin suka rufe iyakokinsu tare da katse hulda da Nijar domin matsa wa sojojin su mika wa Bazoum kujerarsa su koma bariki.

Amma Burkina Faso wadda ita ma sojoji suka kwace mulki ta gaggauta agaza wa takwararta ta Nijar. Wannan kari ne a kan alkawarin taimako ta fuskar soji da Burkina Faso ita da Mali suka yi wa sojojin Nijar akan duk wata barazana ta bangaren.

Daraktan Kwastam na gwamnatin sojin Nijar, Kanar Adamou Zaroumeye ya tabbatar cewa “manyan motoci kimanin 300  na abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum sun iso” sojoji sun iso birnin Yamai da rakiyar sojoji daga kasar Burkina Faso.

Daya daga cikin direbobin motocin, Seydou Mie Zanaidou, ya ce sun dauko kayan daga yankin Kaya da ke Burkina Faso zuwa Dori da ke gabashin kasar sannan suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar ta garin Tera zuwa Yamai.A makon da ya gabata ne dai Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa tankunkumin da aka kakaba wa Nijar da kuma rufe iyakokin kasar sun kawo cikas ga jigilar abinci da magunguna zuwa kasar.