Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta ba wa Wakilin Majalisar Dinkin Duniya wa’adin awa 72 ya fice daga kasar.
Gwamnatin ta ta umarci Louise Aubin, “ya bi duk hanyar da zai bi ya tabbatta ya bar Nijar kafin cikar wa’adin na awa 72.”
- Rikicin Gaza: Jirgin sojin Amurka mafi girma ya tafi Isra’ila
- ’Yan bindiga sun kashe dagaci sun sace jama’arsa a Neja
Umarnin ficewar babban jami’in, wanda aka nada a 2021, na zuwa ne bisa zargin sa da janyo tarnakin da gwamanin sojin ke fuskanta wajen samun karbuwar a Majalisa Dinkin Duniya.
Wa’asin nasa na zuwa ne washegarin da rukuni na biyu na sojojin Faransa suka bar Nijar kamar yadda gwamnatin ta bukata.
A ranar ce kuma Amurka ta yanke tallafinta Dala miliyan 500 da ta ke ba wa Nijar saboda juyin mulkin sojojin.
Idan ba a manta ba, wakilin gwamnatin sojin Nijar ya samu tangarda a Babban Taron MDD karo na 75, wadda Sakatare-Janar na Majalisar, Antonio Guterres ya bayyana a matsayin dalilin rashin halarcin Nijar da taron.
Tuni dai gwamatin ta soki matakin da cewa zai iya kawo cikas ga kokarin sasanta rikicin Nijar.
Wakilin Nijar a MDD kafin juyin mulkin, Bakary Yaou Sangare, shi ne ministan harkokin wajen kasar wanda gwamnatin sojin ta tura ya wakilci kasar a taron.
Sai dai wata majiya ta ce hambararriyar gwamnatin Mohamed Bazoum ta tura wakilinta, wanda a sakamkon haka Majalisar ba ta ba wa Nijar damar halartar taron ba.
Taron shi ne irinsa na farko bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli da sojoji suka yi wa Bazoum, wanda har yanzu yake tsare a hannunsu.
Idan za a iya tunawa a watan Disamban 2022, gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Burkina Faso makwabciyar Nijar ta kori Barbara Manzi, takwaran Louise Aubin, saboda yin gaban kansa wajen janye jami’an MDD daga birnin Ouagadougou.