✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ne dan kwallo na farko a kulob din Panathinaikos daga Najeriya – Abduljalil Ajagun

Abduljalil Ajagun, matashin dan kwallo ne da yanzu haka tauraruwarsa ke haskakawa.  Ya yi wa kulob din Dolphins na Fatakwal wasa sannan ya buga wa…

Abduljalil Ajagun, matashin dan kwallo ne da yanzu haka tauraruwarsa ke haskakawa.  Ya yi wa kulob din Dolphins na Fatakwal wasa sannan ya buga wa kungiyoyin U-17 da U-20 kafin ya tafi kasar Greece inda yake buga wa kulob din Panathinaikos a yanzu.  Aminiya ta samu tattaunawa da shi inda ta ji tarihinsa da kalubalen da ya fuskanta da kuma nasarar da ya samu a harkar kwallo.  Ga yadda hirar takasance:

Zan so ka gabatar mana da kanka?
Ajagun: Sunana Abduljalil Ajagun.  Ina zaune a Tudun Wada Kaduna.  Ni Bayarbe ne kuma shekaruna 23.
Ko za ka bayyana mana tarihin kwallonka?
Ajagun: Na fara ne da kwallon layi, watau inda muke haduwa da abokai da ’yan uwa muna buga kwallo a unguwa daga nan sai na yi wa  kulob din Aminuwa Babes da ke Tudun Wada Kaduna kwallo daga nan na koma kulob cin City Mars shi ma da ke Tudun Wada daga nan ne kuma na wuce wani kulob da ake kira Elcuzero.  To daga nan ne likkafa ta yi gaba inda na tafi kulob din Dolphins da ke Fatakwal na yi musu kwallo.  Na koma Dolphins ne a shekarar 2006 zuwa 2008.  Daga nan ne kuma aka gayyace ni kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) inda na buga mata kwallo.  Sannan daga nan kuma aka sake gayyata ta zuwa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20).  To daga nan ne na zarce zuwa Greece inda babban kulob din Panathinaikos FC ya dauke ni don buga masa kwallo. A shekarar 2013 ce na samu nasarar zuwa kulob din Panathinaikos kuma har yanzu a can nake kwallo.
Wace nasara ka samu a kulob din?
Ajagun: A shekarar farko da na fara yi musu kwallo mun samu nasarar hayewa gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) bayan mun buga wasan neman gurbi (Play-off).  Sannan mun samu nasararllashe kofin kalubale na kasar (FA).
Ya za ka kwatanta rayuwar Turai da ta Najeriya?
Ajagun: Gaskiya da farko na dan fuskanci wahala don irin kwallon ba iri daya ba ce da ta gida Najeriya sannan a lokacin ba na jin yaren girka, ganin cewa yare ne da ban taba jin ana yi ba kafin in koma kasar, don haka sai na kasance bako. Ta kai ba na iya yin magana sai da dabara (irin ta kurame) amma daga baya na koya.  Kamar yadda Hausawa ke cewa ne, kowa ya bar gida, to gida zai bar shi.
To an koya maka yaren ne a can ko yaya abin yake?
Ajagun:  Akwai makarantar da aka kebe don koya wa ’yan kwallo yare, amma mutum yana da zabin zuwa ko a’a.  Amma ni a wasu lokuta ina halarta amma kuma a wani lokaci da kaina na koyi wadansu abubuwa.
A bangaren biyanka hakkoki a kulob din, kana samun matsala?
Ajagun:  Gaskiya ban samu wata matsala wajen biyana albashi da wadansu hakkoki a kulob din ba.
To yanayin kayan wasa fa?
Ajagun: Gaskiya akwai kayayyakin yin wasa a wadace, kama daga riguna da wanduna da takalman kwallo da filin kwallo mai kyau da sauransu, duk wadannan abubuwa da na lissafa maka ba mu da matsalarsu a kulob din.
To bangaren karatu fa?
Ajagun: Na yi karatun sakandare ne kawai, kuma tun da na kare ban cigaba ba sai na tsunduma harkar kwallo.
Me ye ra’ayinka game da dauko wa kungiyar Super Eagles koci daga waje?
Ajagun:  Ba na goyon bayan a dauko wani koci daga waje ba, hasalima a bar ’yan gida su cigaba da nuna basirar da Allah Ya hore musu.  Don haka a ba Salisu Yusuf, kocin riko na Super Eagles na yanzu damar ya horar da kungiyar.
Mene ne burinka a harkar kwallon kafa?
Ajagun:  Babban burina shi ne in yi wa kugiyar Super Eagles kwallo kamar yadda kowane dan kwallo yake da burin yi wa kasarsa kwallo.
kwallaye nawa ka samu nasarar zurawa a raga tun bayan da ka koma kulob din Panathinaikos?
Ajagun:  Na zura kwallaye 20 a gasar rukuni-rukuni na kasar da kuma a kofin kalubale (FA).
Kana da burin ka auri Bsaturiya?
Ajagun:  A gaskiya ba ni da burin auren baturiya ko wata kalar fatar da ba irin ta Najeriya ba.  Hasalima na auri ’yar gida ce kimanin watanni biyu da suka wuce.  Ma’ana na yi tuwoma maina ne a wajen auren ’yar gida.
Wace nasara ka samu a harkar kwallo?
Ajagun: Na samu nasarar lashe gasar rukunin firimiya ta Najeriya a kulob din Dolphins sannan mun kasance na biyu a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) baya ga nasarrar da na samu a kulob din Panathinaikos kamar yadda na fada a baya.
Wane kalubale ka taba fuskanta a harkar kwallo?
Ajagun:  An taba cire sunana a kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20)  bayan mun fita waje don yin wasa.  Kuma wannan abun ya zo mini ne ba-zata, don haka ba zan taba mantawa da shi ba.
Wane bangare kake yin kwallo a cikin fili?
Ajagun: Ina yin wasa ne  a tsakiyar fili (attacking midfielder).
Wace shawara za ka ba matasa masu tasowa?
Ajagun:  Su yi hakuri, kada su ce za su yi gaggawa, su bi komai sannu a hankali.
Wane ne gwaninka a ’yan kwallon duniya?
Ajagun:  Messi da Ronaldo.
Wane kulob ka fi kauna?
Ajagun:  Arsenal da ke Ingila.
 Kai kadai ne bakin fata a kulob din Panathinaikos?
Ajagun:  Mu uku ne amma dai ni kadai na daga Najeriya. Akwai wani daga Kamaru sai  Micheal Essien dan Ghana da ya koma kulob din a bara.  Ka ga mu uku kenan daga Nahiyar Afirka.
To ya batun nuna bambancin launin fata?
Ajagun:  Komai yana tafiya a daidai a Girka, ba sa nuna mana bambancin launi.