Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce shi kadai ne zai iya kwato wa jam’iyyar PDP mulki daga APC muddin ta ba shi takarar Shugaban Kasa a 2023.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron tuntuba da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Jihar Binuwa, da ya gudana a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Makurdi ranar Lahadi.
- Abubuwa 10 da jawabin Buhari ya tabo a Babban Taron APC
- An fasa aure bayan amarya ta gano angonta na da sanko
Wike, wanda ya kuma shaida musu aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasar a hukumance, ya roki goyon bayan daliget din da za su yi zabe daga Jihar.
Ya ce, “In dai ana son a kori PDP daga mulki, to ni kadai ne zan iya nuna wa APC yatsa. Dole mu kwace mulkin nan, kuma a shirye nake. Allah yana tare da mu, dalili ke nan da kullum APC take nuna gazawarta.
“Ina bayyana aniyata ta tsayawa takara a karon farko a hukumance a nan jihar Binuwai. Zan tsaya takarar Shugaban Kasa,” inji Wike.
Ya kuma ja kunnen masu ruwa da tsakin jam’iyyar a jihar da kada su kuskura su sayar da kuri’unsu.
Gwamnan ya kuma zargi wasu ’yan takarar da cewa sun fice daga PDP a baya a shekarar 2015, lamarin da ya sa ta rasa gwamnati, amma yanzu sun sake dawowa neman takara.