Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce yana da kyakkyawar alaka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A watan Agustan da ya gabata, yayin da ake tunkarar zaben 2023, Shekarau ya raba gari da Kwankwaso, wanda shi ma tsohon gwamnan Kano ne.
- Janye tallafin mai: An tashi baran-baran a tattaunawar gwamnati da ’yan kwadago
- Shugaban EFCC, Bawa, na ganawa da Tinubu a Aso Rock
Shekarau ya fice daga jam’iyyar APC a watan Mayu ya koma jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso, amma ya fice daga jam’iyyar a cikin watan.
Yayin da Shekarau ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, Kwankwaso kuma yana jam’iyyar NNPP.
Da ake hira da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Shekarau ya yarda cewa yana da sabanin ra’ayi na siyasa kan wasu batutuwa da Kwankwaso.
Sai dai a cewarsa duk da sabanin ra’ayi irin na siyasa, su aminan juna ne.
“Mu abokai ne sosai. Idan yana magana za ka dauka muna da sabanin ra’ayin siyasa. Mun samu sabani kan batutuwan siyasa da dama.
“Amma hakan ba yana nufin muna fada ba ne, (ko) mu makiya ne. Mu ne abokai ne,” in ji shi.
A yayin tattaunawar, ya yi watsi da yiwuwar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa.
Ya kuma yi magana kan shirin gwamnati mai ci na cire tallafin man fetur, inda ya ce ba ya adawa da hakan.
Jigon na jam’iyyar PDP, ya ce abin da ya faru a fadin kasar nan bai kamata ya zama abin mamaki ba saboda yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cire tallafin mai.
Shekarau ya yi imanin cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da tsarin inganta rayuwa tare da tabbatar da cewa an samar da hanyoyin magance illar cire tallafin man fetur din.