✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ban caccaki Atiku ba – Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da kuma na Turanci, Rahama Sadau ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta caccaki tsohon mataimakin…

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da kuma na Turanci, Rahama Sadau ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan martanin da ya mayar wa Shugaba Muhammad Buhari na cewa matasan Najeriya ’yan cima zaune ne.

A cikin wata sanarwa da jaruma ta aiko wa Aminiya a yau Laraba, ta bayyana cewa ita ba ta zabi wani dan takara a zaben shugaban kasa na 2019 mai zuwa ba, duk da cewa tana da ’yancin yin hakan a matsayinta na ’yar kasa.

Jarumar wadda ta taka muhimmiyar rawa a cikin fim din ‘Sons of the Caliphate’ mai dogon zango da ake nunawa a gidan talabijin na Ebony, ta bayyana cewa cikin takaici ne ta rubuta sakonta don ta karyata batun jita-jitar da ake yadawa cewa ta caccaki jam’iyyar PDP ko kuma wadansu daga cikin ’yan takararta da ke neman shugabancin kasar nan.

Jarumar ta ce, tana alfahari da kasancewarta ’yar Najeriya, kuma tana da ’yancin fadar albarkacin bakinta da kuma na zabe kamar kowa, amma ba tsarinta ba ne ta bayyana ra’ayinta a siyasa ta hanyar kalaman cin fuska ko batanci.

Rahama Sadau wadda ta fito a manyan fina-finan Hausa da suka haxa da ‘Rariya’ da ‘Shakka’ da kuma ‘Kanwar Dubarudu’ ta bayyana bakin cikinta kan yadda waxansu mutane ke yaxa jita-jita ba tare da tabbatar da sahihanci labarin daga wurinta ba.

Ta ce, “Ba ni da wata jam’iyya, ban kuma zabi wani dan takara ba, ba na kuma wata kungiya da ta jibanci siysasa ko cikin wata tafiya ta siyasa, ina so in sanar da mutane cewa ban yi hira da wata kafar yada labarai dangane da labarin da ake yadawa ba. Babu wani abu na labarin da ake yadawa da yake gaskiya.”

Jarumar ta bukaci al’umma cewa kada su yarda da labarin da suka gani ana yadawa, sannan ta gargadi wadanda suka kirkiro labaran da su daina bata mata suna.

“Ina kira ga kafafen yada labarai da su tsaya a kan aikinsu kamar yadda ka’idojin aikin jarida ya shimfida, sannan duk wani abu da suka gani an alakanta shi da ni, to su rika tuntuba ta don su tabbatar da sahihancinsa ko akasin hakan. Na gode, Allah Ya yi muku albarka.” Inji jarumar.