✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF za ta hukunta ’yan kwallon Falcons

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Mista Amaju Pinnick ya sha alwashin hukunta daukacin ’yan kwallon kafa na mata da aka fi sani da…

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Mista Amaju Pinnick ya sha alwashin hukunta daukacin ’yan kwallon kafa na mata da aka fi sani da Super Falcons wadanda suka lashe kofin Afirka na mata a karshen makon jiya saboda boren da suka yi na kin gabatar da kofin da suka lashe ga hukumar har sai an biya su hakkokinu. Wannan mataki da ’yan kwallon suka dauka na rashin gabatar da kofin bai yi wa Hukumar dadi ba, hasalima tamkar sun kunyata hukumar ne a idon duniya.

Duk kokarin da hukumar ta yi na lallashin ’yan kwallon abin ya ci tura don rahotanni sun tabbatar ya zuwa shekaranjiya Laraba ’yan kwallon ba su gabatar da kofin ga NFF ba.
Rahotanni sun nuna wannan abu da ’yan kwallon suka yi tare da jami’ansu zai iya janyo musu matsala, watakila ma a kore su gaba daya don maye gurbinsu da sababbin ’yan wasa.
Rahoton ya ce, Hukumar ta fi zargin ’yan kwallon gaba a kulob din Frnacisca Ordega da laifin ingiza yan kwallon wajen yin bore don haka ake ganin watakila hukumar ta dauki matakin hukunta ta don ya zama darasi ga sauran.
“Zan yi duk mai yiwuwa a karkashin shugabancina na ga ba a sake gayyatar Francisca Ordega a kungiyar Falcons ba har abada”, inji shugaban NFF kamar yadda wata majiya ta kalato yana fadi.
“Za a yi waje rod da akalla ’yan wasan Falcons 10 tare da jami’ansu kuma hukumar NFF za ta fito da sabuwar doka a kan yadda za a rika tafiyarda harkokin kungiyar nan gaba”, inji NFF.
Idan za a tuna ’yan kwallon Falcons sun shiga bore ne jim kadan bayan sun lashe kofin Afirka na mata a Kamaru a karshen makon jiya, al’amarin da ya sa suka yi garkuwa da kofin saboda kin biyansu hakkokinsu. Hukumar NFF ta yi duk mai yiwuwa wajen lallashin ’yan kwallon don su gabatar mata da kofin Afirka da suka lashe amma abin ya ci tura. Haka kuma an ruwaito ’yan kwallon sun ki karbar tayin Naira dubu 100 kowannensu da hukumar ta yi musu a matsayin somi-tabi da niyyar biyansu sauran hakkokinsu idan an samu kudi nan gaba nan amma ’yan kwallon suka yi ki yarda da wannan tayi.
Har zuwa hada wannan rahoton ’yan kwallon ba su janye boren da suke yi ba.