Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta nada tsohon dan wasan Najeriya, kuma tsohon Kyaftin din kasar nan, Joseph Yobo a matsayin Mataimakin Kocin Super Eagles.
Yobo zai maye gurbin Imama Amapakabo, inda zai ci gaba da aiki tare da kocin Super Eagles, Gernot Rohr.
Tsohon dan wasan, ya buga wa kungiyoyi da dama a ciki da wajen Najeriya, ciki har da Eberton, inda ya fi dadewa kuma ya fi yin suna har ya kai ga zama Kyaftin.
Ya buga Gasar Kofin Afirka sau 6, a shekarun 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da 2010 da 2013.
Shi ne Kyaftin din Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe Kofin Afirka a shekarar 2013.
A Super Eagles, Joseph Yobe ya buga wa Najeriya wasa 100. Ba ya ga wasannin da ya buga wa Najeriya a wasannin ’yan kasa da shekara 20.
A shekarar 2001 ne ya fara buga wa Super Eagles, inda ya taka leda a wasan Najeriya da Zambiya a garin Chingola a watan Afrilun shekarar.
Ya kuma halarci gasar Kofin Duniya sau uku, a shekarun 2002 da 2010 da 2014.
Haka kuma ya buga wa Olympikue Marseille ta Faransa, da Fenerbahce ta Turkiyya da Norwich City ta Ingila.
Joseph Yobo mai shekara 39 ya fara wasa ne da kungiyar Michelin ta garin Fatakwal a Jihar Ribas, inda daga baya ya fice daga kasar nan, inda ya buga wa kungiyar Standar Liege ta Belgium kafin likafarsa ta yi sama.