✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta nada Jose Peseiro sabon kocin Super Eagles

Zai fara jagorantar Super Eagles a ziyarar da za ta kai Amurka a wasannin sada zumunci.

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF ta sanar da nada Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.

Hukumar ta ce Jose Peseiro mai shekara 62 wanda dan asalin kasar Portugal ne shi zai jagoranci tawagar Super Eagles.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin NFF Ademola Olajire ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Sanarwar ta ce zai fara jagorantar tawagar Super Eagles a ziyarar da za ta kai Amurka a wasannin sada zumunci.

Tsohon dan wasan Super Eagles Finidi George da Salisu Yusuf za su zama mataimakan sabon kocin.

Tun a watan Disamba Hukumar Kwallon Najeriya ta fara sanar da nada kocin amma daga baya ta nada Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwarya domin ya ja ragamar Super Eagles a gasar cin kofin Afirka.

A watan Disamban 2021 NFF ta ce kwamitin zartarwata ne ya amince da nada Peseiro kuma zai zama mai sa ido kafin a dawo ya ci gaba.

Amma daga baya hukumar ta ce ta fasa saboda kwazon Augustine Eguavoen.

Jose Peseiro wanda tsohon kocin kungiyar Sporting Lisbon da Porto ne, ya horar da Venezuela da Saudiyya.

Ya horar da kungiyoyi a Afirka da kasashen Larabawa da suka hada da Al ahly ta Masar da Al Hilal ta Saudiyya.