✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta kara wa Kocin Eagles Rohr shekara 2

Hukumar shirya kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta kara tsawaita kwantaragin shekara biyu ga kocin Super Eagles Gernot Rohr. Hukumar NFF ta ce tuni ta…

Hukumar shirya kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta kara tsawaita kwantaragin shekara biyu ga kocin Super Eagles Gernot Rohr.

Hukumar NFF ta ce tuni ta gama biyan kocin basussukan da yake bin ta bashi na shekarar 2017 don karfafa masa gwiwar ci gaba da horar da kungiyar ba tare da wata matsala ba.

Shugaban Hukumar NFF Mista Amaju Pinnick ne ya sanar da haka ga menama labarai a Legas a ranar Litinin da ta wuce.  Ya ce da ma kocin ya kulla kwantaragin horar da Super Eagles ne na tsawon shekara biyu a shekarar 2015 don haka yanzu da kwantaraginsa ta kare ne aka sake kara masa wasu shekaru biyu wanda sai a shekarar 2019 sabon kwantaragin za ta kare.

 Idan za a tuna kocin ne ya samu nasarar hayewa da Super Eagles gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi.

Hukumar ta ce yanzu ta karkata akalarta ne wajen samo Naira biliyan 2 da za ta yi amfani da su don halartar gasar cin kofin duniya a Rasha.