✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar ya zama dan kwallon da ya fi daukar albashi a duniya

dan wasan kungiyar Barcelona da ke kasar Spain kuma dan asalin kasar Brazil, Neymar ya zama dan wasan kwallon kafa na duniya mafi daukar albashi…

dan wasan kungiyar Barcelona da ke kasar Spain kuma dan asalin kasar Brazil, Neymar ya zama dan wasan kwallon kafa na duniya mafi daukar albashi a duniya bayan da ya sanya hannu a sabon kwantaraginsa da kungiyar ta Barcelona.
Jaridar Marca da ake bugawa kullum a Spain ta ruwaito cewa, da wannan dan wasan gaban ya kawo karshen rade-radin da ake yadawa kan makomarsa a kungiyar, kuma sabon kwantaragin Neymar zai rika amsar albashin Fam miliyan 25 (kimanin Naira biliyan 11 da miliyan 250) a shekara bayan an cire haraji, inda ya doke Lionel Messi da ke karbar Fam miliyan 22 a shekara.
An kuma sanya wasu yarjejeniyoyi masu muhimmanci a sabon kwantaragin nasa da zai kare a shekarar 2012.  An kiyasta darajar kwantaragin a kan Fam miliyan 200 a shekarar farko, sai Fam miliyan 222 a shekara ta biyu da kuma fam miliyan 250 a shekara ta uku ta karshe.
dan wasan, kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da PSG da Manchester United da kuma Real Madrid sun yi ta kai-komon zawarcinsa don ya buga musu wasa kafin ya sanya hannu da Barcelona.
dan wasan, ya dade yana fana cewa yana jin dadin buga wa kungiyar Barcelona wasa kuma ba ya son barin kungiyar.