✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar ya tsallake rijiya da baya

Shahararren dan kwallon Brazil da ke buga wa kulob din FC Barcelona na Sifen kwallo Neymar ya tsallake rijiya da baya a ranar Lahadin da…

Shahararren dan kwallon Brazil da ke buga wa kulob din FC Barcelona na Sifen kwallo Neymar ya tsallake rijiya da baya a ranar Lahadin da ta wuce bayan ya gamu da mummunan hadarin mota a kan hanyarsa ta zuwa filin wasa.
An ce dan kwallon ya gamu da hatsarin ne a lokacin da yake kokarin zuwa filin wasa don ya hadu da takwarorinsa na kulob din Barcelona ana gab da yin wasan La-Liga a tsakanin kulob din Real Sociedad da na Barcelona.
An tashi wasan ne da ci 1-1 kuma Neymar ne ya yi sanadiyyar ba Messi kwallon da ya rama cin da Sociedad din ta yi musu tun da farko, da hakan ya sa aka tashi wasan 1-1.
Sai dai rahoton ya nuna dan kwallon ya auna arziki, tun da duk da hstarin da ya rutsa da shi bai yi ko kwarzane ba, hasalima yana daga cikin ’yan kwallon da suka fafata a wasan.
Kulob din FC Barcelona ne ya sanar da aukuwar hatsarin a shafin sadawarsa na Twitter inda ya nuna “Neymar ya gamu da hatsari a motarsa amma ya auna arziki bai ji ciwo ba, kuma muna fata dan kwallon zai buga wasanmu da Real Sociedad”.
Motar Neymar da ya yi hatsari da ita, an kiyasta kudinta a kan Fam dubu 200 kwatankwacin Naira miliyan 115.
Da yawa daga cikin magoya bayan Barcelona ba su ji dadin yadda wasan ya kaya ba, ganin yadda kulob din Real Sociedad ya yi biji-biji da na Barcelona a wasan.  Kawo yanzu kulob din Real Madrid ya ba na Barcelona tazarar maki 6 ne a teburin gasar inda a gobe idan Allah Ya kaimu za a kece raini a tsakanin kulob din da na Real Madrid a wasa mafi zafi da ake masa lakabi da El-clasico.