✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar ya ji rauni

Shahararren dan kwallon kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa Neymar, a shekaranjiya Labara ne ya sake jin rauni a duddugen kafarsa da hakan…

Shahararren dan kwallon kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa Neymar, a shekaranjiya Labara ne ya sake jin rauni a duddugen kafarsa da hakan ta sa da wuya in zai iya buga wasan zakarun kulob na Turai a tsakanin kulob dinsa da na Manchester United da ke Ingila a ranar Talata 12 ga watan gobe.

Neymar dai ya ji raunin ne a lokacin da kulob din PSG yake fafatawa da na Strasbourg a gasar cin kofin kalubale na Faransa wato Coupe de France.

A daidai minti na 62 aka ga Neymar yana dindigishi da hakan ya sa aka canza shi.  PSG ce ta samu nasara a wasan da ci 2-0, inda Edison Cabani da Di Maria suka zura kwallayen.

Ya zuwa hada wannan rahoto kulob din PSG bai sanar da takamaiman lokacin da Neymar zai yi yana jinya kafin ya koma fagen daga ba.