✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NERC ta haramtawa kamfanonin wuta karban sama da Naira 1,800 ga marasa mita

Biyo bayan yawan korafi da al’umma ke yi kan tsadar kudin wuta na kiyasi da kamfanonin rarraba wutar lantarki wato (DisCOs) ke yi a kan…

Biyo bayan yawan korafi da al’umma ke yi kan tsadar kudin wuta na kiyasi da kamfanonin rarraba wutar lantarki wato (DisCOs) ke yi a kan masu amfani da wutar.

Hukumar sa ido a kan al’amuran wutar lantarki ta kasa wato NERC ta haramtawa kamfanonin rarraba wutar da adadinsu ya kai 11 karban kudin wuta a kowane wata da ya haura Naira dubu 1,800 daga abokan huldarsu a bangaren gidaje, har sai ta sa masu mita.

A wata sanarwa na umarni da hukumar ta fitar da ke dauke da sa hannun shugabanta Farfesa James Momoh da Kwamishininta a bangaren dokoki, tabbatar da bin ka’ida da kuma bada lasisi Barista Dafe Akpeneye, hukumar ta NERC ta ce, ta soke dokar shekarar 2012 da ta baiwa kamfanonin damar sa kudin wuta kan tsarin kiyasi, sannan ta ce wannan dokar ta fara aiki tun a ranar Alhamis da ta gabata.

Hukumar ta ce, adadin masu amfanin wutar lantarki a kasar nan ya tashi daga miliyan 5 a shekarar 2012, zuwa miliyan 10 a watan Disamba ta shekarar 2019.