Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, zai ci gaba da zaman da yake yi a kasar waje don neman lafiya har sai abin da hali ya yi.
Sanarwar hakan dai na kunshe ne a cikin wata wasika da Gwamnan ya aike wa Majalisar Dokokin Jihar, ranar Litinin.
- TETFund ta fara amfani da dalibai wajen duba gine-ginenta a manyan makarantu
- Kwamandojin ’yan ta’adda 2 sun mika wuya ga sojoji a Borno
Idan za a iya tunawa, a ranar 5 ga watan Yuni ce Akeredolu ya bar jihar domin neman lafiya da niyyar dawowa ranar 6 ga watan Yulin 2023.
Amma ranar Litinin, Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji, a cikin wata gajeruwar sanarwa ranar Litinin ya tabbatar da cewa Gwamnan zai ci gaba da zaman a can har sai lafiyarsa ta inganta.
Ya ce Gwamnan ya kara wa’adin ne bayan shawarar likita kan ya kara hutawa har sai ya murmure kafin ya dawo.
Ya ce tuni majalisar ta karbi wasikar Gwamnan ta neman kara wa’adin, kamar yadda sashe na 190 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
Wasikar dai ta ce Mataimakin Gwamnan, Lucky Aiyedatiwa ne za ci gaba da rike kujerar a matsayin Mukaddashi, har sai an samu umarni sabanin hakan.