A ci gaba da buga wasannin neman cancantar buga kofin nahiyar Afirka (AFCON), tawagar Najeriya ta Super Eagles ta lallasa takwararta ta Sao Tome and Principe da ci 10 ba ko daya.
A wasan dai wanda aka fafata ranar Litinin, dan wasan Najeriya Victor Osimhen ne ya ci wa Super Eagles kwallo hudu shi kadai.
- Jirgin ruwan Sudan ya nitse da tumaki 15,000 a hanyarsa ta zuwa Saudiyya
- CAN ta gargadi APC kan tsayar da Musulmi 2 a matsayin ‘yan takara
Osimhen ya fara zura wa Najeriya kwallo ta farko ne a minti na tara da fara wasan, kafin ya taimaka wa Moses Simon da Terem Moffi su ma su zura nasu kwallayen a mintuna na 28 da na 43.
Ya kuma kara kwallonsa ta biyu a ragar abokan hamayyar nasu a minti na 48, sannan ya kara ta uku a minti na 65.
Osimhen, wanda dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya ya ci kwallonsa ta hudu ne a minti na 84, lamarin da ya kawo adadin kwallayen da Najeriya ta ci zuwa biyar.
Shi kuwa Terem Moffi ya ci kwallonsa ta biyu ne a minti na 60, sai Oghenekaro Etebo da Dennis Emmanuel da kuma Lokman Ademola su ma suka zuzzura kwallo dai-daya.